Atiku ya yi kaca-kaca da Shugaba Buhari kan watsi da sauya fasalin kasa a jihar Kano

Atiku ya yi kaca-kaca da Shugaba Buhari kan watsi da sauya fasalin kasa a jihar Kano

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma manemin takarar kujerar shugaban kasa karkashin inuwa ta jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi kaca-kaca gami da sukar jam'iyya mai ci ta APC kan watsi da kudirinta na sauya fasalin kasa.

Kamar yadda shafin jaridar Vanguard ta ruwaito, tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan cikin babban birni na Kanon Dabo yayin ganawarsa da manema labarai a kwana-kwanan.

Turakin na Adamawa wanda yana daya daga cikin wadanda suka bayar da muhimmiyar gudunmuwa ta kafa tsare-tsaren sauya fasalin kasar nan tare da yi ma ta garambawul tun a shekarar 1994, ya caccaki gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari kan watsi da wannan kudiri.

Atiku ya kausasa harshe tare da bayyana damuwarsa kan wannan lamari sakamakon rashin cika alkawarin da gwamnatin shugaba Buhari ta kudirta yayin yakin ta na neman zabe a shekarar 2015.

Atiku ya yi kaca-kaca da Shugaba Buhari kan watsi da sauya fasalin kasa a jihar Kano

Atiku ya yi kaca-kaca da Shugaba Buhari kan watsi da sauya fasalin kasa a jihar Kano
Source: Depositphotos

Legit.ng ta ruwaito cewa, a watan Agustan da ya gabata ne mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa, Najeriya ba ta bukatar sauya fasalin ta a halin yanzu yayin wani zaman sauraron ra'ayin al'ummar kasar nan a birnin Minneapolis na kasar Amurka.

Wannan lafazi ko shakka ba bu ya janyo babatu gami da cecekucen ra'ayoyi daga lunguna da sakonni na kasar nan baya ga gudanar muhawarori daga jiga-jigai na kasar nan.

Har ila yau, tsarin sauya fasalin kasar nan tsohon mataimakin shugaban kasar ya takaita ne akan rage nauyin da ya rataya a wuyan gwamnatin tarayya musamman kan harkokin tsaro, shige da fice da kuma harkokin kuɗi da suka shafi babban bankin kasar nan.

KARANTA KUMA: Tarnaki a PDP: Ba bu wanda zan janyewa takarar kujerar shugaban Kasa - Jang

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, tsohon mataimakin shugaban kasar na daya daga cikin 'yan takara 12 dake hankoron tikitin takarar kujerar shugaban karkashin jam'iyyar ta PDP, inda suke sha alwashin goyan bayan duk wani dan takara da jam'iyyar za ta tsayar yayin zaben fidda gwani.

A yayin ziyarar da ya kai birnin na Kano, Atiku ya samu kyakkyawar tarba ta karamci bisa jagorancin shugaban jam'iyya na jihar, Sanata Lawal Jibrin Doguwa da kuma dumbin magoya baya na jam'iyyar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel