Rikicin makiyaya ba kan Buhari farau ba - Osinbajo

Rikicin makiyaya ba kan Buhari farau ba - Osinbajo

- Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa tun kafin shugaban kasa Buhari ya hau mulki ake kashe kashe a fadin kasar

- Osinbajo ya ce an fara ire iren wadannan hare haren tun wajajen shekara ta 1999, wanda ya ci gaba har kawo yanzu

- Ya ce kashe kashen da ake yi ba wai rikicin addini bane, illa dai kawai rikici akan gonakai, wanda yayi sanadin kashe musulmai da dama a jihar Zamfara.

Tun kafin zuwan shekara ta 2015, gabanin hawan shugaban kasa Buhari karagar mulkin Nigeria, akwai jerin gwanon kashe kashe a yankunan Arewa da kudancin kasar, wanda hakan ya faru ne sakamakon rikice rikice akan gonaki da sauran dukiya a tsakanin al'umma.

Osinbajo, mataimakin shugaban kasar Nigeria wanda ya bayyana hakan a Calabar a lokacin da ya ke gabatar da jawabi ga shuwagabanni da malaman majami'u a ranar Talata, ya ce an fara ire iren wadannan hare haren tun wajajen shekara ta 1999, wanda ya ci gaba har kawo yanzu.

"A matsayinmu na gwamnati, muna da nauyin da ya rataya a wuyanmu na kare rayukan Al'umarmu amma ku gane wannan da idon basira, gwamnati kadai ba zata iya magance matsalar da ta ke addabar tsaro ba.

Rikicin makiyaya ba kan Buhari farau ba - Osinbajo

Rikicin makiyaya ba kan Buhari farau ba - Osinbajo
Source: Depositphotos

KARANTA WANNAN: Mai gadi ya shiga halin ha-ula'i bayan da aka kamashi yana cire allunan tallar APC

"A jihar Filato, an fara kashe kashe tun daga 1999 da kuma 2001, an sanya takunkumi, kai har takai an tsige gwamnan da ke shugabanci a lokacin, aka maye gurbinsa da mulkin soja, duk da hakan, rikicin bai tsaya ba har zuwa 2015.

Osinbajo yanbayyana cewa gwamnatin shugaban kasa Buhari, ita ce ta samu nasarar kawo karshen rikicin a shekarar 2015 da ta fara mulki, wanda har aka zarce shekaru 2 babu rikici har sai 2018 rikicin ya dawo.

Ya ce kashe kashen da ake yi ba wai rikicin addini bane, illa dai kawai rikici akan gonakai, dukiya da kuma ruwa, wanda yayi sanadin kashe musulmai da dama a jihar Zamfara.

Da ya ke magana akan ci gaba da tsare Leah Sharibu da yan ta'addan Boko Haram suka yi, mataimakin shugaban kasar ya ce babu wani kyakkyawan tsammanin nasara ko da kuwa anyi yarjejeniya, don haka babu wanda zai iya fadin ranar da zata dawo, ko sauran yan matan Chibok za su dawo.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel