2019: Zamu baku gwamna dake kishin ku – Oshiomhole ga jama’ar jihar PDP a arewa

2019: Zamu baku gwamna dake kishin ku – Oshiomhole ga jama’ar jihar PDP a arewa

- Shugaban APC na kasa, Adams Oshiomhole, ya bukaci jama’ar jihar Taraba su kwantar da hankalinsu domin karshen gwamnatin PDP a jihar ya zo

- A jiya, Litinin, ne Oshiomhole ya rantsar da sabon shugabancin jam’iyyar APC a jihar Taraba karkashin jagorancin Honarabul Ibrahim Tukur El-sudi

- Oshiomhole ya ce APC zata bawa mutanen Taraba gwamna da zai zauna a cikin jihar

Shugaban APC na kasa, Adams Oshiomhole, ya ce jam’iyyar zata bawa mutanen jihar Taraba gwamna da zai zauna a jihar a shekarar 2019.

Oshiomhole ya yi wannan magana ne a jiya, Litinin, yayin rantsar da sabon shugabancin jam’iyyar na jihar Taraba karkashin jagorancin Honarabul Ibrahim Tukur El-Sudi.

Shugaban jam’iyyar ya bukaci sabbin shugabannin da masu ruwa da tsaki da su yi kokari domin ganin APC tayi nasara a zabukan 2019 tare da sanar da cewar APC zata maye gurbin gwamnan jihar, Darius Ishaku, da baya zama a jihar.

2019: Zamu baku gwamna dake kishin ku – Oshiomhole ga jama’ar jihar PDP a arewa

Oshiomhole da Darius Ishaku
Source: UGC

Ina da yakinin cewar jam’iyyar APC karkashin jagorancin El-Sudi tare da goyon bayan jama’a zata kayar da gwamna Darius Ishaku a zaben shekarar 2019.”

DUBA WANNAN: 2019: 'Yan takarar PDP 6 da zargin cin hanci ya hana sukuni

“Daga abinda nake ji daga bakin mutanen jihar Taraba, shine sun gaji da gwamna Darius Ishaku kuma sun zaku zaben 2019 ya zo domin su canja shi. Mu a jam’iyyar APC zamu tabbatar da cewar mun tsayar da dan takara mai kishi da zai zauna tare da jama’a domin yi masu aiyukan da zasu inganta rayuwar su,” a cewar Oshiomhole.

A wani labarin na Legit.ng kun ji cewar kungiyar dillalan man fetur masu zaman kan su (IPMAN), kungiyar direbobi masu dakon man fetur (PTD), kungiyar direbobi (NARTO) da karin wasu kungiyoyi biyu sun sayawa gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufa’i, fam din takara.

Da yake karbar fam din takarar a jiya, Litinin, El-Rufa’i, ya yiwa kungiyoyin godiya tare da shiada masu cewar sun sauke masa nauyi domin ba kankanin tashin hankali ya shiga ba bayan jam’iyyar APC ta fitar da farashin fam din takara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel