APC tayi Magana aka siyan fam din takara da Joshua Dariye yayi daga gidan yari

APC tayi Magana aka siyan fam din takara da Joshua Dariye yayi daga gidan yari

- Jam'iyyar APC tayi Magana aka siyan fam din takara da Joshua Dariye yayi dagagidan yari

- Jam'iyyar tace ba zata taba bari wadda aka kama da laifi yayi takara a karkashinta ba

- Cewa bibiyar jerin sunayen yan takaran da suka biya kudin fam din jihar Plateau bai nuna bayani kan haka ba

Kimanin sa’o’i 24 bayan an yi zargin cewa Sanata Joshua Dariye wadda ke fuskanar daurin shearu 14 a gidan yari ya siya fam din takarar kujerar sanata mai wakiltan Plateau ta tsakiya, APC tayi Magana kan matsayin siyan fam din.

Premium Times ta rahoto cewa jam’iyyar a ranar Talata, 11 ga watan Satumba ta kaddamar da cewa ba zata taba bari kowani tsohon mai laifi ya nemi kowani kujera a karkashinta ba cewa dokar Najeriya da kundin tsarin mulkinta ya haramta zabe duk mutumin da aka samu da hannu dumu-dumu wajen aikata wani laifi.

APC tayi Magana aka siyan fam din takara da Joshua Dariye yayi dagagidan yari

APC tayi Magana aka siyan fam din takara da Joshua Dariye yayi dagagidan yari
Source: Depositphotos

Babban sakataren labarai na jam’iyyar, Yekini Nabena yace babu tabbacin cewa Dariye ya siya fam din takaran, cewa bibiyar jerin sunayen yan takaran da suka biya kudin fam din jihar Plateau bai nuna bayani kan haka ba.

Nabena ya ci gaba da bayanin cewa idan wani yayi nasarar karba masa fam din, za’ayi waje da sunansa cewa ya tuntubi sashin doka na jam’iyyar akan lamarin.

KU KARANTA KUMA: 2019: Ba zamu hakura cikin sauki kamar Jonathan ba – Magoya bayan Atiku

A baya Legit.ng ta ahoto cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata, 11 ga watan Satumba ya bayyana cewa yan siyasa masu rauni sun bar jam’iyyar All Progressives Congress, (APC).

Buhari na hannunka mai sanda ne ga yan siyasa da dama da suka sauya sheka daga jam’iyyar zuwa jam’iyyun adawa.

Yayi maganan ne yayinda ya karbi fam din sake tsayawa takara da kungiyar Nigeria Consolidation Ambassador Network (NCAN) ta siya masa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel