Tarnaki a PDP: Ba bu wanda zan janyewa takarar kujerar shugaban Kasa - Jang

Tarnaki a PDP: Ba bu wanda zan janyewa takarar kujerar shugaban Kasa - Jang

Daya daga cikin manema tare da hankoron tikitin takarar kujerar shugaban kasa karkashin inuwa ta jam'iyyar PDP, Jonah Jang, ya bayyana cewa ba bu wani dan takara da zai janyewa takararsa cikin dukkanin 'yan takara na jam'iyyar.

Kamar yadda shafin jaridar Vanguard ya ruwaito a ranar yau ta Talata, Mista Jang ya kuma bayyana cewa ko jam'iyyar kanta ba ta hurumi ko ikon tursasa shi janye takarar sa a halin yanzu.

Jang, wanda shine Sanatan jihar Filato ta Arewa ya bayyana hakan ne yayin ganarwar sa da manema labarai cikin daular mahallinsa dake unguwar Maitama cikin babban birnin tarayya na Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa, Sanatan ya yi wannan furuci tare da bayyana matsayarsa yayin da yake kan hanyar sa ta zuwa shelkwatar jam'iyyar PDP domin mika takardunsa na bayyana kudirin takara a jam'iyyar.

Tsohon gwamnan na jihar Filato na hankoron tikitin takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar tare da wasu jiga-jigai 12 da suka hadar har da tsohon Mataimakin shugaban kasa; Alhaji Atiku Abubakar, Tsohon gwamnan jihar Kano; Sanata Rabi'u Kwankwaso da kuma tsohon shugaban majalisar dattawa; Sanata David Mark.

Tarnaki a PDP: Ba bu wanda zan janyewa takarar kujerar shugaban Kasa - Jang

Tarnaki a PDP: Ba bu wanda zan janyewa takarar kujerar shugaban Kasa - Jang
Source: Getty Images

Sauran jiga-jigan masu hankoron tikitin jam'iyyar sun hadar da; shugaban majalisar dattawa; Abubakar Bukola Saraki, gwamnan jihar Sakkwato; Aminu Waziri Tambuwal da kuma gwamnan jihar Gombe; Alhaji Ibrahim Dankwambo.

Legit.ng ta ruwaito cewa, jam'iyyar ta kafa wani kwamitin amintattu da zai fara tuntube-tuntube na neman amincewar 'yan takarar jam'iyyar akan kulla yarjejeniyar fidda gwani daya tilo da zai fafata a zaben 2019.

Sai dai da yawan 'yan takarar da suka hadar har da tsohon gwamnan na jihar ta Filato sun ja daga tare da bayyana kudiri gami da furucin duk wanda ya iya Allonsa ya wanke yayin zaben fidda gwani na jam'iyyar kamar yadda dimokuradiyya ta tanadar.

A yayin ganawar sa da manema labarai, Sanata Jang ya kara da cewa, ba ya da nufin janye kudirin sa ga kowane dan takara na jam'iyyar wanda da ba don haka ba da bai mallaki takardar bayyana kudiri ba.

KARANTA KUMA: Saraki, Atiku, Kwankwaso sun ja daga kan tikitin takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP

Cikin tsare-tsaren da tsohon gwamnan ya bayyana muddin ya yi nasarar lashe zaben kujerar shugaban kasa a zaben 2019, ya sha alwashin habaka tattalin arziki, sauya fasalin hukumomi masu hana yiwa tattalin arziki zagon kasa gami da yakar cin hanci da rashawa.

Tsohon gwamnan wanda a halin yanzu ke fuskantar dambarwar zargin aikata laifin rashawa, ya kalubalanci shugaban kasa Muhammadu Buhari kan gazawarsa ta fuskar tsare-tsare da fasalin hukumomi masu yaki da cin hanci da rashawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel