Yan siyasa mafi rauni sun bar APC – Inji Shugaba Buhari

Yan siyasa mafi rauni sun bar APC – Inji Shugaba Buhari

- Shugaba Buhari ya bayyana cewa yan siyasa masu rauni sun bar jam’iyyar

- Ya bayyana hakan ne yayinda ya amshi fam din tazarce da wata kungiya ta siya masa

- Yace wadanda suka bar jam’iyyar bazasu iya sanya ra’ayin kasa a gaba da son zuciyarsu ba wadda shine kan gaba a manufofin gwamnatin

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata, 11 ga watan Satumba ya bayyana cewa yan siyasa masu rauni sun bar jam’iyyar All Progressives Congress, (APC).

Buhari na hannunka mai sanda ne ga yan siyasa da dama da suka sauya sheka daga jam’iyyar zuwa jam’iyyun adawa.

Yayi maganan ne yayinda ya karbi fam din sake tsayawa takara da kungiyar Nigeria Consolidation Ambassador Network (NCAN) ta siya masa.

Yan siyasa mafi rauni sun bar APC – Inji Shugaba Buhari

Yan siyasa mafi rauni sun bar APC – Inji Shugaba Buhari
Source: Depositphotos

A cewarsa, wadanda suka bar jam’iyyar bazasu iya sanya ra’ayin kasa a gaba da son zuciyarsu ba wadda shine kan gaba a manufofin gwamnatin.

KU KARANTA KUMA: 2019: Ba zamu hakura cikin sauki kamar Jonathan ba – Magoya bayan Atiku

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai karbi fam din sa na sake tsayawa takara a karkashin Jam’iyyar sa ta APC mai mulki a zabe mai zuwa na 2019.

Idan ba ku manta ba, wata Kungiya ce mai ra’ayin Shugaban ta cire kudi har Naira Miliyan 45 ta saya masa fam domin ya nemi zarcewa kan kujerar sa. Wannan Kungiya ta saye fam din ne lokacin Shugaban kasar yana can Kasar China.

Wasu manyan Lauyoyi dai sun bayyana cewa bai halatta ‘Yan takara su karbi gudumuwar da ta haura Naira Miliyan guda ba. Sai dai wannan Kungiya ta biyawa Shugaban kasar kudin fam din Miliyoyi duk da ana tunani ya sabawa dokar kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel