2019: Nine gaba da Atiku, ba zan janye masa ba - Lamido

2019: Nine gaba da Atiku, ba zan janye masa ba - Lamido

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya mayar da martani ga wani jawabi wadda tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar yayi na cewa, Lamido zai janye masa daga tseren shugaban kasa.

Dukkaninsu su biyun na neman tikitin babban jam’iyyar adawa na Peoples Democratic Party (PDP) tare da wasu yan takara guda goma.

A wani taro tare da shugabannin PDP a Dutse, jihar Jigawa a ranar Litinin, 10 ga watan Satumba, Mista Abubakar yace yayi imani cewa Lamido zai janye masa a matsayinsa na yayansa.

Yace yayi imani Mista Lamido zai mara masa baya wajen samun tikiti saboda tsohon gwamnan ya kasance kaninsa kuma suna da tunanin siyasa iri guda.

2019: Nine gaba da Atiku, ba zan janye masa ba - Lamido

2019: Nine gaba da Atiku, ba zan janye masa ba - Lamido
Source: Depositphotos

Da yake mayar da martani ga furucin Atiku a ranar Talata, 11 ga watan Satumba ta bakin hadiminsa, Adamu Usmna, Mista Lamido yace ba zai janye masa ba.

KU KARANTA KUMA: Kasancewa matashi kadai bai isa da za’a ba mutun shugabanci ba - Oshimhole

“Zancen gaskiya Atiku ya grime mania a shekaru, amma ni yayansa ne a siyasance saboda na kasance a majalisar wakiulai a 1979 lokacin da shi ya kasance ma’aikaci a hukumar kwastam.

“Sannan idan shekaru ne abun dubawa wajen tsayawa zabe toh shi ma ya janye ma Buhari.”

A cewar Usman, Lamido ya dade yana hakuri da biyayya ga PDP don haka idan ma akwai wanda za’a janyewa toh shi yakamata a janyemawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel