Takarar Saraki a PDP na fuskantar tarnaki, ya ce ba zai janye ba

Takarar Saraki a PDP na fuskantar tarnaki, ya ce ba zai janye ba

- Shugaban majalisa, Bukola Saraki ya ce ba zai janye wa wani dan takarar a jam'iyyar PDP ba

- Saraki ya shawarci kwamitin zartarwa na PDP ta rungumi zabe fidda gwani saboda kowa tashi da fice shi

- Saraki ya gargadi mahukunta a PDP da su guji yin wani abinda zai raraba kan 'yan jam'iyyar

Shugaban majalisar dattawa kuma daya daga cikin masu neman takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar PDP, Dr. Bukola Saraki ya ce ba zai amince ya janye wa wasu 'yan takarar ba duk da yunkurin da kwamitin amintatun na jam'iyyar keyi na zaban dan takara guda.

Takarar Saraki a PDP na fuskantar tarnaki, ya ce ba zai janye ba

Takarar Saraki a PDP na fuskantar tarnaki, ya ce ba zai janye ba
Source: Depositphotos

A hirar da ya yi da manema labarai a sakatariyar PDP da ke Abuja, bayan ya mayar da takardar tsayawa takararsa, Saraki ya ce abinda ya dace shine a bawa 'yan takarar dama su kece raini a zaben fidda gwani.

DUBA WANNAN: Fadan sarkin musulmi tayi tsokaci kan hatsarin 'dan Sultan

Tsohon gwamnan na jihar Kwara, ya shawarci Kwamitin Zartarwa na jam'iyyar tayi adalci wajen shirye-shiryen zaben na fidda gwani saboda dan takarar da yafi cancanta ya samu tikitin takarar jam'iyyar.

"Ba zancen tsayar da dan takara daya bane a gaban mu saboda muna kokarin tabattar da inganta demokradiyar cikin gida da tabbatar da yin zaben fidda gwani da 'yan jam'iyya za su gamsu dashi. Abinda ke da muhimmanci shine gudanar da abinda kowa zaiyi na'am da shi.

"A halin yanzu muna aike tare saboda dukkanmu 'yan gida daya ne. Na san cewa zamu amince da hanyar fitar da dan takarar da kowa zai bashi goyon baya. Saboda haka babu bukatar raba kawunan mu," inji Saraki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel