Ambode zai sake neman takarar Gwamna a Jam’iyyar APC

Ambode zai sake neman takarar Gwamna a Jam’iyyar APC

Gwamna Akinwunmi Ambode na Jihar Legas ya saye fam din sake takarar kujerar Gwamnan Jihar inda yake neman goyon bayan Jama’a su mara masa baya su sake zaben Jam’iyyar APC a 2019.

2019: Gwamna Ambode zai sake neman takarar Gwamna a Jam’iyyar APC

Gwamna Ambode ya saye fam din takarar Gwamna a APC
Source: Twitter

A farkon makon nan Akinwunmi Ambode yayi watsi da duk wata jita-jita na cewa zai fice daga APC ya yanki fam din neman tazarce a kan karagar mulki. Gwamnan ya taka ne zuwa Hedikwatar Jam’iyyar APC a Garin Abuja ya saye fam.

Gwamnan ya nuna hoton sa ne tare da wasu manyan APC irin su Shugaban gudanarwa na Jam’iyyar watau Hon. Emma Ibediro da kuma babban Lauyan APC na kasa Babatunde Ogala da wasu manyan Jam’iyyar a babban Hedikwatar APC.

KU KARANTA: Buhari ya karbi fam din sake takarar Shugaban kasa

A baya an ta rade-radin cewa Gwamnan ne Legas zai fice daga APC kafin zaben 2019. Gwaman dai karyata wannan labari inda yace yana nan a Jam’iyyar APC mai mulki. Yanzu dai Gwamnan ya soma neman goyon bayan mutanen Legas.

Ambode ya nuna cewa yayi wa Legas aiki tukuru a cikin shekaru 3 da yayi yana Gwamna don haka yake neman a cigaba da mara masa baya a 2019. Wani Sanatan Jihar ya bayyana cewa tsohon Gwamna Tinubu yana tare da Gwamnan na yanzu.

Dazu kun ji cewa wasu ‘Yan kasuwa sun nuna takaicin su da aka shan gaban su wajen sayawa Shugaba Muhammadu Buhari fam. Kawo yanzu dai an sayawa Gwamnonin Kaduna, Kano da Neja fam domin su cigaba da zarcewa kan kujerun su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel