Kwamishina yayi murabus don tsayawa takarar gwamnan jihar Ogun

Kwamishina yayi murabus don tsayawa takarar gwamnan jihar Ogun

- Otunba Bimbo Ashiru, kwamishinan kasuwanci da masa’antu, ya ajiye mukaminsa don tsayawa takakarar gwamnan jihar Ogun

- A safiyar yau ne ya rubuta takardar ajiye aiki don maida hankali kan kudirinsa na tsayawa takarar gwamnan jihar

- Otunba Ashiru ya bukaci goyon baya daga al’umar jihar, don cika burinsa na kawo ci gaba a jihar baki daya

Otunba Bimbo Ashiru, kwamishinan kasuwanci da masa’antu, ya ajiye mukaminsa don tsayawa takakarar gwamnan jihar Ogun, inda zai kara da mai gidansa gwamnan jihar na yanzu, Ibikunle Amosun.

Rahotanni sun bayyana cewa Ashiru wanda ya kasance a matsayin kwamishinan da ya dade a cikin mukarraban gwamnan, ya yi murabus don yin takara, bayan da ya sayi fam din nuna sha’awarsa ta tsayawa takara karkashin jam’iyyar APC a ranar 25 ga watan Satumba.

Tsohon kwamishinan, dan asalin garin Ijebu-Ode da ke a mazabar Ogun ta Gabas, ya shaidawa manema labarai tabbacin murabus dinsa, inda ya godewa gwamnan da daukacin al’umar jihar Ogun bisa damar da suka bashi na yiwa kasar haihuwarsa aiki a matsayin kwamishina.

KARANTA WANNAN: Gwamnan jihar Rivers ya zargi shugaba Buhari da kitsa tuggun kawar dashi daga duniya

Gwamna Amosun na fuskantar kalubale bayan da kwamishinansa ya fito takarar kujerarsa a APC

Gwamna Amosun na fuskantar kalubale bayan da kwamishinansa ya fito takarar kujerarsa a APC
Source: Facebook

Ashiru ya ce: “Eh kwarai, gaskiya ne na rubuta takardar ajiye aikina a safiyar yau don maida hankali kan kudirina na tsayawa takarar gwamnan jihar. Idan baku manta ba, tun a shekarar da ta gabata, al’umar yankin Ijebu suka tsayar da ni dan takararsu na gwamna. Sune kuma suka saya min fam din takarar kujerar karkashin jam’iyyar APC.

“Don haka, yan zamar min wajibi na amsa kiran al’umar Ijebu-Remo na yiwa jihata aiki a matsayin gwamna idan na samu nasara, kuma a matsayina na dan kwarai, ya zamar min dole in ajiye aikina don mayar da hankali kan zaben fitar da gwamani, kamar yadda jam’iyyarmu ta APC ta bada umurni,” a cewarsa.

Daga karshe, Otunba Ashiru ya bukaci goyon baya daga daukacin al’umar jihar Ogun, na ganin ya cika burinsa na kawo ci gaba a jihar baki daya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel