Kujerun Sanata da gwamnoni sun fara hada fada a jihohi, tsakanin gwamnoni da Sanatoci

Kujerun Sanata da gwamnoni sun fara hada fada a jihohi, tsakanin gwamnoni da Sanatoci

- An dai maida talakawa sha-ka-tafi ne, inda zaka ga gwamna da Sanata da Minista suna musayar kujerunsu a jiha daya, kamar babu wani wanda ke da iko ko damar lekawa ciki.

- Tun daga 1999 har izuwa yanzu, kamar dai har yanzu tsakaninsu suke musayar kujeru

- Tsohon gwamnan ya Kwatanta rahoton da karya, yace Kato bayan Kato kadai zai tabbatar da hakan

Kujerun Sanata da gwamnoni sun fara hada fada a jihohi, tsakanin gwamnoni da Sanatoci

Kujerun Sanata da gwamnoni sun fara hada fada a jihohi, tsakanin gwamnoni da Sanatoci
Source: Depositphotos

Ban mikawa Geidam tikitin kujerar sanatan Yobe ta yamma ba. Zaben fidda gwani na Kato bayan Kato kadai zai iya ba wa mutum tikitin. Wannan damokaradiyya ce.

Tsohon gwamnan jihar Yobe, Sanata Bukar Ibrahim, yace bai mika tikitin kujerar Sanata ga Gwamna Ibrahim Geidam ba. Ibrahim ya bayyana hakan ne a lokacin da yake maida martanin rahoton da aka bada ta yanar gizo,a garin Damaturu.

Tsohon gwamnan ya Kwatanta rahoton da karya, yace Kato bayan Kato kadai zai tabbatar da hakan.

Yace damokaradiyya akeyi kuma ita mukeyi a jam'iyyar mu ta APC. Mutane ne zasu tantance, kuma suna da damar zaben ra'ayin su.

DUBA WANNAN: Kudin da aka raba a wata shida na 2018

An dai maida talakawa sha-ka-tafi ne, inda zaka ga gwamna da Sanata da Minista suna musayar kujerunsu a jiha daya, kamar babu wani wanda ke da iko ko damar lekawa fadar mulki.

Tun daga 1999 har izuwa yanzu, kamar dai har yanzu tsakaninsu suke musayar kujeru.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel