Sept. 11th: Amurka na tuna yau a matsayin ranar makokin hare-haren 'yan ta'adda

Sept. 11th: Amurka na tuna yau a matsayin ranar makokin hare-haren 'yan ta'adda

- Shekaru 17 kenan da aka kaiwa Amurka hari

- Hare-haren dai kungiyar Al-Qaida ta Usama Bin Laden ce ta kaisu

- Harin ya sauya tsarin duniya gaba daya

Sept. 11th: Amurka na tuna yau a matsayin ranar makokin hare-haren 'yan ta'adda

Sept. 11th: Amurka na tuna yau a matsayin ranar makokin hare-haren 'yan ta'adda
Source: Depositphotos

A 2001, a rana mai kamar ta yau, an kai hare-haren ta'addanci mafi girma a duniya, wadanda suka sauya duniya baki daya, suka kuma tayar da yake-yake da har yau ba'a gama su ba, kuma miliyoyi suka mutu, a kowanne bangare.

Hare-haren, an gano kungiyar ta'addanci ta Al-Qaida, wadda Usama bin laden ya hada, ita ke da alhakin kai harin, a biranen New York da Washington, inda aka yi asarar mutane akalla 3,000, da jikkata wasu dubbai, sai kuma asarar kudi da aka kiyasta sun kai dalar Amurka Tiriliyan daya.

DUBA WANNAN: Barazanar Boko Haram na qaruwa

Yakin da wannan hari ya jawo, ya haifar da sabuwar damara da Amurka da qawayenta suka dauka, inda ta kai har aka kai hari Afghanistan, aka kori 'yan Taliban daga mulki, aka dora gwamnati ta zamani ta dimokuradiyya.

Su dai Taliban, karkashin Mulla Omar, sun baiwa su Oama bin Laden mafaka ne, shi yasa aka hada har dasu.

An kashe Usama shekaru 10 bayan harin, a Pakistan, bayan yayi zaman buya da gujewa shari'a, sai dai kafin ya rasu, ya riga ya farkar da yawa daga masu zafin ra'ayin addini su dauki kamai su tayar da jihadi a kasashensu.

Wannan shi ya kai har a Najeriya aka sami kungiyoyi masu goyon bayan irin nasa kishin addinin, suka tayar da yaki, wadannan su ake kira Boko Haram.

Kasashen Larabawa ma na can suna fama da irin nasu masu tayar da qayar bayan, na gaba-gaba sune ISIS.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel