Karin Albashi: Gwamnati bata shirya biya ba - NLC

Karin Albashi: Gwamnati bata shirya biya ba - NLC

- Gwamnatin tarayya bata shirya tabbatar da karancin albashi

- Tun watan Nuwamba na 2017 aka kafa kwamitin amma sai watan Maris 2018 ya fara aiki

- Sunce basu tsaida takamaiman albashin ba

Karin Albashi: Gwamnati bata shirya biya ba - NLC

Karin Albashi: Gwamnati bata shirya biya ba - NLC
Source: Depositphotos

Shugaban kungiyar kwadago ta kasa, Ayuba Wabba, ya zargi Gwamnatin tarayya da ministan kwadago, Sanata Chris Ngige da tsayar da karin karancin albashin, yace ma'aikata bazasu cigaba da hakuri ba.

Ansan cewa zuwa 21 ga watan Augusta na zasu kammala aikin da kwamitin karin karancin albashin, amma sai Ministan Kwadago yace Gwamnatin tarayya bata shirya ba.

"Hakan na nuna cewa basu shirya tabbatar da karin karancin albashin ba a ranar 4 da 5 ga watan satumba, duk da mu dai mun kammala shirye shiryen mu " inji Wabba.

" Za'a iya tunawa cewa, an nada kwamitin ne tun a watan Nuwamba 2017 amma basu fara aiki ba sai a watan Maris, akan dalilin da su kadai suka sani."

DUBA WANNAN: Barazanar Boko Haram na qaruwa

Kamar yanda tsarin aikin ya nuna, yakamata mu kammala ne zuwa 21 ga watan Augusta, amma sai ya fada a ranar hutu Hakan yasa aka maida zuwa 4 da 5 ga watan Satumba.

A wannan taron ne yakamata mu kammala dukkan rahoto, sannan mu kawo karshen aikin. Amma kafin mu kammala sai ministan kwadago, a matsayin wakilin Gwamnatin tarayya ya tashi yace suna da bukata tataunawa kafin su tsayar da karancin albashin. Inji Wabba

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel