2019: Surukin Buhari ya sayi fam din takarar gwamna

2019: Surukin Buhari ya sayi fam din takarar gwamna

- Dakta Mahmood Ahmed, surukin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sayi fam din takarar neman gwamna a jihar Adamawa karkashin jam’iyyar APC

- Yayin kaddamar da takarar sa a jiya, Yola ta cika makil da dubban magoya bayansa da suka haddasa cunkuso a manyan hanyoyin garin

- Wani abu da ya tayar da hankalin hadimai da magoya bayan gwamna Jibrilla shine yadda Ahmad ya dauki hoto tare da shugaba Buhari bayan sayen fam din takara a ranar Juma'a

Dakta Mahmood Ahmed, surukin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sayi fam din takarar neman gwamna a jihar Adamawa karkashin jam’iyyar APC.

Da yake magana da manema labarai jiya, Litinin, a Yola, Ahmad, kani ga Aisha Buhari, ya ce gwamnatocin baya a Adamawa basu yi rawar gani ba wajen inganta rayuwar jama’a da kawowa jihar cigaba ba.

Yayin kaddamar da takarar sa a jiya, garin Yola ya cika makil da dubban magoya bayansa da suka haddasa cunkuso a manyan hanyoyin garin da zasu kai ga ofishin jam’iyyar APC.

Zamu kawo cigaba jihar Adamawa ta hanyar shimfida aiyuka da inganta rayuwar jama’a. Zamu bayar da kwangilar aiyuka ga ‘yan kwangilar mu na gida domin habaka kasuwanci,” a kalaman Ahmad.

Batun takarar ta Ahmad na cigaba da tayar da kura a tsakanin magoya bayan gwamna Umaru Jibrilla da kuma fagen siyasar jihar Adamawa.

2019: Surukin Buhari ya sayi fam din takarar gwamna

Shugaba Buhari a wurin taron jam'iyyar APC
Source: Facebook

Wani abu da ya tayar da hankalin hadimai da magoya bayan gwamna Jibrilla shine yadda Ahmad ya dauki hoto tare da shugaba Buhari bayan sayen fam din shin a takara.

Magoya bayan gwamnan na ganin cewar Ahmad na iya samun sahalewa da goyon bayan shugaba Buhari a zaben shekarar 2019.

A kwanakin baya ne Legit.ng ta kawo maku labarin cewar a wani sabon salon siyasa, kungiyoyi biyu sun sayawa dan takarar gwamna a jihar Adamawa, Dakta Mahmood Ahmad, fam guda biyu tare da kai masa su har gidansa dake unguwar Maitama a Abuja.

DUBA WANNAN: 2019: 'Yan takarar PDP 6 da zargin cin hanci ya hana sukuni

Da yake karbar fam din da kungiyoyin suka saya masa, Ahmed ya ce, “ina mika godiya ga abokaina da suka bani mamaki ta hanyar saya min fam din takara saboda maganar gaskiya na karaya bayan uwar jam’iyya ta fitar da farashin fam din takara.”

Mambobin jam’iyyar APC da dama sun yi korafi a kan tashin gwauron zabi da farashin fam din takarar kujeru daban-daban ya yi amma duk da hakan masu son yin takarar na ruge-rugen sayen fam dinsu na tsayawa takara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel