Kasancewa matashi kadai bai isa da za’a ba mutun shugabanci ba - Oshimhole

Kasancewa matashi kadai bai isa da za’a ba mutun shugabanci ba - Oshimhole

Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Adams Oshiomhole ya fadama matasan Najeriya da kada su kwana da tunanin cewa shekarun kadai zai yantasu wajen samun shugabanci.

Oshiomhole ya fadi hakan a wani hira da yayi da gidan talbijin din Channels a Abuja, a daren ranar Litinin, 10 ga watan Satumba.

Yana martani ne akan wata tambaya game da tsadar fam din nuna ra’ayin tsayawa takara.

A cewarsa don mutun ya kasance matashi ba yana nufin zai fi iya rike mulki bane, cewa kamata yayi matasa su fara sanin yadda ake tafiyar da abu tukuna.

Kasancewa matashi kadai bai isa da za’a ba mutun shugabanci ba - Oshimhole

Kasancewa matashi kadai bai isa da za’a ba mutun shugabanci ba - Oshimhole
Source: Depositphotos

Yace ba wai shugabanci kawai ya kamata matasa su mayar da hankali ba cewa su fara sanin yadda ake tafiyar da harkokin kasuwanci da dai sauransu, amma ba wai su fara da mutane ba.

KU KARANTA KUMA: 2019: Dasuki ya shiga tseren takarar gwamna a Gombe

Ya bayar da misali da shugabannin Facebook da na’urar Apple cewa matasa ne amma basu yi karanci da zama biloniya ba.

Oshiomhole ya jadadda cewa mutanen da suka fi kudi a duniya a yanzu mafi yawancinsu matasa ne masu kwazo da tunani.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel