Shugaba Buhari ya yi jaje ga gwamnati da mutanen jihar Nasarawa kan fashewar gas

Shugaba Buhari ya yi jaje ga gwamnati da mutanen jihar Nasarawa kan fashewar gas

- Shugaba Buhari mika sakon jaje gwamnati da mutanen jihar Narsarawa akan fashewar iskar gas

- Hakan na kunshe ne a wata sanarwa daga Garba Shehu

- Buhari ya bukaci hukumomin gwamnati da masu ruwa da tsaki su taimakawa wadanda suka ji rauni sannan ya roki Allah ya ji kan wadanda suka mutu

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi jaje ga gwamnati da mutanen jihar Narsarawa akan mumunan lamari na tashin gobara da iskar gas ya haddasa a tashar gidan mai dake Lafia, babban brnin jihar wadda yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

Sakon jajen shugaban kasar na kunshe ne a wani jawabi daga babban mai bashi shawara a kafofin watsa labarai, Malam Garba Shehu a Abuja, a ranar Litinin, 10 ga watan Satumba.

Fashewar gas din ya afku ne a kusa da gidan man fetur, inda akalla mutane 10 suka mutu, sannan sama da mutane 30 suka ji raunuka daban-daaban, sannan kuma motoci da shaguna da dama suka kone.

Shugaba Buhari ya yi jaje ga gwamnati da mutanen jihar Nasarawa kan fashewar gas

Shugaba Buhari ya yi jaje ga gwamnati da mutanen jihar Nasarawa kan fashewar gas
Source: Depositphotos

Shugaban kasar wadda aka sanarma irin barnan rayuka da dukiya da lamarin yayi, ya nuna kulawa sosai da juyayi akan lamarin.

KU KARANTA KUMA: Digiri na 3 da Gwamna Ortom ya mallaka na jabu ne – Akume

Ya yi ta’aziya ga iyalan wanda abun ya shafa sannan ya roki hukumomin jiha da na tarayya da masu fada a aji a jihar da tabbatar da bayar da taimakon ingantattun magunguna ga wadanda suka samu rauni.

“Ina roko da fatan kada irin wannan mumunan lamari ya sake faruwa a kowani yanki na kasar,” inji shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel