'Yan Najeriya sun aminta da riƙon amanar mu - INEC ga PDP

'Yan Najeriya sun aminta da riƙon amanar mu - INEC ga PDP

Mun samu cewa hukumar zabe ta kasa watau INEC tare da jam'iyya mai ci ta APC, sun mayar da martani ga gwamnonin jam'iyyar adawa ta PDP kan zargin su akan shirye-shirye da kulla kitimurmura da aiwatar da magudi yayin zaben 2019.

A yayin mayar da martani hukumar ta bayyana cewa, 'yan Najeriya sun aminta da ita wajen tabbatar da gaskiya gami da adalci yayin gudanar da zaben a badi, inda a halin yanzu ta ke ci gaba da kai kawo domin tabbatar da gudanar zaben cikin inganci da aminci.

Kakakin shugaban hukumar, Mista Rotimi Oyekanmi, shine ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai cikin babban birnin kasar nan na tarayya a ranar Litinin din da ta gabata.

'Yan Najeriya sun aminta da riƙon amanar mu - INEC ga PDP

'Yan Najeriya sun aminta da riƙon amanar mu - INEC ga PDP
Source: Depositphotos

Kazalika jam'iyyar ta APC ta mayar da wannan martani da sanadin kakakin ta na kasa, Mista Yekini Nabena, yayin ganawar sa da manema labarai na jaridar The Punch cikin birnin na Abuja a ranar da ta gabata.

KARANTA KUMA: Ba mu da tabbaci kan rikon amanPar Hukumar INEC - Gwamnonin PDP

Mista Nabena ya kuma yi watsi da ikirarin gwamnonin jam'iyyar ta adawa kan cewa jam'iyyar APC ta shiga cikin al'amurra tare da yin kakagida akan harkokin hukumar INEC domin cimma manufofin ta.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, kungiyar gwamnonin ta jam'iyyar PDP bisa jagorancin shugabanta gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, na ci gaba da zargi gami da tuhumar gwamnatin tarayya da shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da jam'iyyar sa ta APC kan kulla kitimurmura ta magudi da kuma cin karen su ba babbaka yayin zaben 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel