Ba mu da tabbaci kan rikon amanar Hukumar INEC - Gwamnonin PDP

Ba mu da tabbaci kan rikon amanar Hukumar INEC - Gwamnonin PDP

Gwamnoni ma su rike da kujerun mulki a kasar nan karkashin jam'iyyar PDP, sun debe tsammani tare da fidda rai kan tabbacin amanar hukumar zabe ta kasa watau INEC dangane da tabbatar da gaskiya da kuma adalci yayin gudanar da zaben 2019.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ta ruwaito, gwamnonin su na zargin cewa gwamnatin tarayya da kuma jam'iyyar mai ci ta APC sun riki hukumar INEC a matsayi wani makamin na cin karen su ba babbaka kan duk wasu harkokin gudanar da zabe a kasar nan.

Rahotanni sun bayyana cewa, gwamnonin su na tuhuma kai tsaye ga shugaban hukumar zaben, Farfesa Mahmud Yakubu da kuma babbar kwamishina ta hukumar, Hajiya Amina Zakari, wajen aiwatar da duk wani ruwa da tsaki na rashin gaskiya kan harkokin zabe.

Ba mu da tabbaci kan rikon amanar Hukumar INEC - Gwamnonin PDP

Ba mu da tabbaci kan rikon amanar Hukumar INEC - Gwamnonin PDP
Source: Depositphotos

Legit.ng ta fahimci cewa, gwamnonin sun cimma wannan matsaya ne yayin wani taron ganawa a tsakaninsu da suka gudanar cikin babban birnin kasar nan na tarayya a daren ranar Lahadin da ta gabata.

Shugaban kungiyar gwamnonin jam'iyyar ta adawa kuma gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, shine ya rattaba hannu kan wannan matsaya a madadin takwarorin sa yayin tarion da aka gudanar a fadar gwamnatin sa dake birnin Asokoro a garin Abuja.

KARANTA KUMA: Zaben fidda gwani: An fara rikici tsakanin Gwamnoni da Shugaban jam'iyyar APC

Baya ga wannan tuhuma, gwamnonin sun kuma kausasa harshe dangane da yadda gwamnatin tarayya ke amfani da hukumomin tsaro wajen cimma manufofin ta na siyasa, inda ta buga misali da zamba da magudin zabe da ta auku a jihohin Ekiti, Osun da kuma jihar Ribas.

Kazalika gwamnonin sun bayyana rashin jin dadin su dangane da rashin amincewar shugaban kasa Muhammadu Buhari kan sabuwar doka ta sauya fasalin gudanar da zabe a kasar nan

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel