2019: INEC za ta hada kai da ICPC domin hukunta masu sayan kuri'u

2019: INEC za ta hada kai da ICPC domin hukunta masu sayan kuri'u

- Hukumar ICPC za ta hada gwiwa da INEC domin magance matsalar sayan kuri'u

- ICPC ta ce dokan kasa ya bata ikon hukunta masu rashawa ciki har da wanda suka aikata rashawar lokacin zabe

Hukumar yaki da rashawa da laifuka masu alaka da rashawa mai zaman kanta (ICPC), ta ce a shirye ta ke tayi aiki tare da hukumar zabe na kasa (INEC), domin magance mastalar sayan kuri'u a lokacin gudanar da zabe.

Mukadashin Ciyaman din ICPC, Mr Musa Abubakar, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a yayin da ya ziyarci Ciyaman din INEC, Farfesa Mahmood Yakubu a ofishinsa da ke Abuja a ranar Litinin.

Za'a dauki matakan hukunta masu sayan da kuri'u

Za'a dauki matakan hukunta masu sayan da kuri'u
Source: Depositphotos

Abubakar ya ce kudin tsarin mulkin Najeriya ya bawa ICPC ikon gudanar da bincike da a kan laifukan da suka shafi rashawa har da wadanda aka aikata lokacin jefa kuri'a.

DUBA WANNAN: Fadan sarkin musulmi tayi tsokaci kan hatsarin 'dan Sultan

A bangarensa, shugaban INEC, Farfesa Yakubu, ya yabawa ICPC game da kokarin ta na yin hadin gwiwa tare da INEC domin magance matsalar sayan kuri'u.

Ya ce INEC a shirye ta ke domin daukan duk wani mataki na tabbatar da cewa sayan kuri'u ba zai kawo cikas a babban zaben 2019 da za'a a gudanar ba.

"Kuri'un da mutane suka jefa ne zai nuna wanda zaiyi nasara a zaben. Muna mayar da hankali domin ganin cewa mun dakile hanyoyin da masu sayan kuri'u ke amfani da shi.

"Masu jefa kuri'a ne za su zabi wanda zaiyi nasara amma muna da alhakin tabbatar da cewa hakan ya faru ba tare da saba doka ba," inji shi.

Ya kubu ya kuma ce bayan hadin gwiwa da ICPC da EFCC, INEC za ta dauki wasu matakai na musamman domin tabbatar da cewa babu wanda ya saya kuri'u musamman a ranar da ake gudanar da zabe.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel