Abin da ya sa ban bari Matasan da ke kokarin neman na abinci sun saya mani fam ba – Shehu Sani

Abin da ya sa ban bari Matasan da ke kokarin neman na abinci sun saya mani fam ba – Shehu Sani

Sanatan Kaduna ta tsakiya a Majalisar Dattawa Shehu Sani ya bayyana yadda ya hana Jama’a saya masa fam din sake takara karkashin Jam’iyyar ta APC mai mulki a zabe mai zuwa na 2019. Fam din takarar kujerar Sanata dai ya kai kusan Naira Miliyan 8.

Abin da ya sa ban bari Matasan da ke kokarin neman na abinci sun saya mani fam ba – Shehu Sani

Sanata Shehu Sani yace ya hana Matasa saya masa fam din takara
Source: Twitter

Shehu Sani yayi wani jawabi a shafin sa na sadarwa na zamani na Tuwita inda ya bayyana cewa wasu Matasa sun yi kokarin saya masa fam din takara amma ya hana su. Sanatan yace bai amince da wannan tsari na yaudara a siyasa ba.

A jiya ne mu ka ji cewa an sayawa Gwamnan Kaduna da wasu Gwamnonin APC fam din takara 2019. Shi dai ‘Dan Majalisar na tsakiyar Jihar Kaduna ya nuna cewa ba ya tare da sauran ‘Yan siyasar da ke yaudarar al’umman kasar.

KU KARANTA: Wata Kungiya ta ciji yatsa bayan an riga ta sayawa Buhari fam din takara

Sanata Shehu Sani yace Matasan da su kayi yunkurin saya masa fam din takarar su na kokarin neman na-kan-su ne don haka ya ki amincewa da rokon da su ka kawo masa na sayan fam din takarar Sanatan Yankin sa a madadin sa.

Kafin nan dai Sanatan ya caccaki Atiku Abubakar wanda yayi kuka lokacin da zai karbi fam din sa na takarar Shugaban kasa. Sanatan yace babu abin da zai sa shi kukan karya domin shi ‘Dan siyasa ne ba mai shirya wasan kwaikwayo ba.

Kun ji cewa wasu ‘Yan kasuwan Jihar Neja sun sayawa Gwamnan Jihar Abubakar Sani Bello fam din tsayawa takara a zaben 2019. A Jihar Kano ma dai wasu sun sayawa Gwamna Abdullahi Ganduje fam din domin ya zarce kan kujerar sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel