Ministan Najeriya na neman biyan wasu Lauyoyi Biliyan 7 a iska bayan an karbo kudin Abacha

Ministan Najeriya na neman biyan wasu Lauyoyi Biliyan 7 a iska bayan an karbo kudin Abacha

Wani babban Lauya na kasar waje da Gwamnatin Najeriya tayi haya domin karbo mata wasu kudin Kasar da ake zargin tsohon Shugaba Sani Abacha ya sace ya boye a Luxembourg ya zargi Ministan shari’a da kokarin yin ba daidai ba.

Ministan Najeriya na neman biyan wasu Lauyoyi Biliyan 7 a iska bayan an karbo kudin Abacha

Ana rikici kan Dala Miliyan $321,000,000 da aka maidowa Najeriya
Source: Depositphotos

Enrico Monfrini ya nuna cewa Ministan shari’a na Najeriya Abubakar Malami SAN na kokarin canza bayanin Miliyoyin kudin da Najeriya ta samu ta karbo daga kasar waje. Ministan na kokarin biyan wasu Lauyoyi bayan an karasa aikin.

Jaridar The Cable ta rahoto cewa Ministan shari’a na kasar watau Malami yana kokarin biyan wasu Lauyoyin Najeriya; Oladipo Okpeseyi da Temitope Adebayo Naira Biliyan 7 da sunan aiki bayan an kamalla dawowa Najeriya da kudin ta.

KU KARANTA: An bankado karyar da Gwamnatin Najeriya ta shirga

A baya dai mun ji cewa Gwamnatin Jonathan tayi alkawarin biyan Lauyan kasar wajen Enrico Monfrini bangare cikin kudin aikin sa. Sai dai shi Minista Abubakar Malami SAN ya nuna cewa sam bai ji dadin wannan yarjejeniya ba.

Babban Lauyan na kasar waje yayi wa Ministan raddi inda yace kudin sa shi ne kashi 5% na abin da aka karbo ya kuma nuna cewa babu wata bukatar a sake biyan wasu Lauyoyi kudin aiki domin kuwa ya kammala duk abin da ake bukata.

Lauyan na waje da Najeriya tayi haya a baya Enrico Monfrini, ya tabbatar da cewa ya gama duk abin da ake bukata a Kotu wajen dawowa Najeriya da wannan kudi don haka babu dalilin lale Dala Miliyan 17 a ba wasu Lauyoyin Najeriya kuma.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel