Rikici ya kunno kai a Jam'iyyar PDP sakamakon wani sabon hukunci da ta yanke

Rikici ya kunno kai a Jam'iyyar PDP sakamakon wani sabon hukunci da ta yanke

- Jam'iyyar PDP ta bukaci yan takararta da su biya wasu kudade da suka kama daga N200,000 zuwa Miliyan biyu, don yin gyare gyare a ofishinta

- Yan takara a shiyyar Kudu maso Gabas, karkashin PDP, na ci gaba da nuna fushinsu a fili, sakamakon hukuncin da jam'iyyar ta dauka

- Sai dai mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa da ke a shiyyar, Deacon Austin Umahi ya ce ba wai haraji bane aka dorawa yan takarar

Yan takara a shiyyar Kudu maso Gabas, karkashin jam'iyyar PPD, na ci gaba da nuna fushinsu a fili, sakamakon hukuncin da ofishin shiyya na jam'iyyar ya dauka, wanda suka misalta shi da kora da hali daga kudirinsu na tsayawa takara karkashin jam'iyyar.

Jam'iyyar PDP a shiyyar ta bukaci yan takararta da su biya wasu kudade na daban, da suka kama daga N200,000 zuwa Miliyan biyu, don baiwa jam'iyyar damar yin gyare gyare a ofishinta na shiyya da ke Independence Layout, Enugu.

Sai dai mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa da ke a shiyyar, Deacon Austin Umahi ya ce ba wai haraji bane aka dorawa yan takarar, illa dai wasu yan kudaden shiga da jam'iyyar ta ke son tarawa don tafiyar da ayyukanta

Rikici ya kunno kai a Jam'iyyar PDP sakamakon wani sabon hukunci da jam'iyyar ta yanke

Rikici ya kunno kai a Jam'iyyar PDP sakamakon wani sabon hukunci da jam'iyyar ta yanke
Source: Twitter

Umahi ya ce, "Ba wai muna karbar haraji bane. Muyi duban tsanaki akan wannan lamarin, hukumar jam'iyyar ta shiyya, sun yi wani zama a ofishin jam'iyyar da ke Enugu inda ana nan ne suka cimma matsaya na umurtar yan takara bada tallafi don gudanar da ayyukan jam'iyyar.

KARANTA WANNAN: Kungiyar kwadago ta zargi gwamnatin tarayya da kin cika alkawarin karawa ma'aikata albashi

"A taron, dukkanin hukumomin sun yi na'am da wannan shawara, kuma kowa ya sanya hannu akai. PDP jam'iyya ce da ke gudanar da ayyukanta akan tsari, don haka, babu wani mutum daya tilo da ya isa ya dora haraji akan yan takara."

Bisa rahotannin da jaridar Vanguard ta tattara, ta gano cewa taron wanda Umahi ya jagoranta, ofishin shiyyar ya umurci dukkanin yan takara da biyan wasu kudade do yin gyare gyare a ofishin.

Kowane dan majalisar dokoki na jiha mai ci a yanzu, zai biya N200,000, yayin da masu neman tsayawa takarar kujerar zasu biya N100,000. A bangaren yan majalisun wakilai na tarayya da ke ci a yanzu, za su biya Naira miliyan daya yayin da masu neman kujerar za su biya N500,000.

Sanatoci masu ci a yanzu zasu biya Naira miliyan biyu, yayin da masu neman kujerar za su biya Naira miliyan daya. Gwamnoni masu ci a yanzu kuwa za su biya N5m, yayinda yan takarar kujerar za su biya Naira miliyan daya.

Sai dai wannan hukunci na jam'iyyar bai yiwa yan takarar dadi ba, inda wasu suka bayyana fushinsu a fili.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel