Kaka-kara-kaka: Kamfanin MTN ya maka ministan Buhari kotu, yana neman hakkin sa

Kaka-kara-kaka: Kamfanin MTN ya maka ministan Buhari kotu, yana neman hakkin sa

- Kamfanin MTN ya maka ministan Buhari kotu, yana neman hakkin sa

- Kamfanin a ranar Litinin din da ta gabata ne ya shigar da karar

Kamfanin sadarwar nan na MTN a Najeriya ya maka babban bankin na Najeriya watau Central Bank of Nigeria (CBN), da kuma Antoni Janar na kasar kuma ministan shari'a a gwamnatin shugaba Buhari kotu yana neman a bi masa hakkin sa.

Kaka-kara-kaka: Kamfanin MTN ya maka ministan Buhari kotu, yana neman hakkin sa

Kaka-kara-kaka: Kamfanin MTN ya maka ministan Buhari kotu, yana neman hakkin sa
Source: Original

KU KARANTA: Ba maganar karin alawus da masu yiwa kasa hidima

Kamar dai yadda muka samu, shi dai kamfanin a ranar Litinin din da ta gabata ne ya shigar da karar kotu a garin Abuja, yana kalubalantar matakin da gwamnatin Najeriya ta kakaba masa.

Legit.ng ta samu haka zalika cewa mai magana da yawun kamfanin ya kara da cewa matakin da suka dauka ya zama dole ne saboda su kare kan su, kadarorin su da ma sauran abokan huldar su.

Idan dai mai karatu bai manta ba a kwanan baya ne gwamnatin tarayya ta ci tarar kamfanin na MTN wasu zunzutun kudade saboda samun su da sukayi da laifin keta dokokin kasa da aka shata masu.

A wani labarin kuma, Fadar shugaban kasar Najeriya karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari a ranar Litinin din da ta gabata ta bayyana cewa babu batun na'urar nan ta tantance katin zabe a cikin daftarin gyararren tsarin zaben 2018 da majalisa ta aikewa shugaban kasar.

Wannan ne ma dai ya sanya fadar ta ce rashin maganar na'urar da wasu 'yan matsaloli ne ma ya sa shugaba Muhammadu Buhari ya ki sanya hannu a kan kudurin dokar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel