2019: Buhari ya karbi fam din takarar da aka saya masa

2019: Buhari ya karbi fam din takarar da aka saya masa

Mun samu labari cewa dama ana sa rai cewa yau ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai karbi fam din sa na sake tsayawa takara a karkashin Jam’iyyar sa ta APC mai mulki a zabe mai zuwa na 2019.

2019: Buhari zai karbi fam din takarar da aka saya masa

Buhari da masu neman bayan takarar sa a 2018
Source: Depositphotos

A Ranar Talatan yau dinnan ne aka shiya cewa Shugaban kasa Buhari zai amshi fam din da aka saya masa domin ya sake neman takara a zaben 2019. Mai magana da yawun Shugaban kasar watau Malam Garba Shehu ya bayyana wannan.

A jiya Garba Shehu ya sanar da ‘Yan jarida cewa tabbas yau Shugaban kasar zai yi hannu da fam din sake neman takarar sa a fadar Shugaban kasa na Aso Villa da ke babban Birnin Tarayya Abuja bayan an fansan masa fam din a makon jiya.

KU KARANTA: Ban da Miliyan 20 a banki - Gwamna El-Rufai

Idan ba ku manta ba, wata Kungiya ce mai ra’ayin Shugaban ta cire kudi har Naira Miliyan 45 ta saya masa fam domin ya nemi zarcewa kan kujerar sa. Wannan Kungiya ta saye fam din ne lokacin Shugaban kasar yana can Kasar China.

Wasu manyan Lauyoyi dai sun bayyana cewa bai halatta ‘Yan takara su karbi gudumuwar da ta haura Naira Miliyan guda ba. Sai dai wannan Kungiya ta biyawa Shugaban kasar kudin fam din Miliyoyi duk da ana tunani ya sabawa dokar kasar.

Dazu kun ji cewa wasu ‘Yan kasuwan Jihar Neja sun nuna takaicin su da aka shan gaban su wajen sayawa Shugaba Muhammadu Buhari fam. Ana dai bude saida fam din ne wannan Kungiya tayi wuf ta sayawa Buhari domin nuna goyon-baya.

Yanzu haka wannan Kungiya ta mutanen da ke kokarin ganin Shugaba Buhari ya cigaba da aikin da ya faro a Najeriya sun mika masa fam din takaran 2019 a ofishin sa da ke fadar Shugaban kasan a Aso Villa a babban Birnin Tarayya Abuja.

Ga dai bidiyon nan kamar yadda Shugaban kasar ya nuna a shafin sa na Facebook

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Mailfire view pixel