Kungiyar kwadago ta zargi gwamnatin tarayya da kin cika alkawarin karawa ma'aikata albashi

Kungiyar kwadago ta zargi gwamnatin tarayya da kin cika alkawarin karawa ma'aikata albashi

- Kungiyar kwadago ta kasa NLC ta bayyana cewa gwamnatin tarayya bata da wata niyyar sake fasalin mafi karancin albashin ma'aikata a kasar

- Shugaban kungiyar NLC Comrade Ayuba Wabba ya ce hukuncin da gwamnatin tarayya ta yanke zai tilastawa kungiyar zama a mako mai zuwa don yanke nata hukuncin

- Ministan kwadago, ya ce gwamnati bata shirya karin albashi mafi karanci ga ma'aikatan kasar a yanzu ba, har sai sun kammala sabuwar tuntuba

Kungiyar kwadago ta kasa NLC ta bayyana cewa gwamnatin tarayya bata da wata niyyar sake fasalin mafi karancin albashin ma'aikata a kasar, duk da cewa ta yi alkawarin yin haka tare da nuna bukatar karawa ma'aikata albashin su.

A wannan gabar, kungiyar ta shirya kiran wani gagarumin taron kusoshinta a mako mai zuwa, don tattara rahotanni akan gwamnatin tarayya tare da daukar mataki na gaba "don tabbatar da cewa ba'a tauye bukatun ma'aikata ba."

Shugaban kungiyar NLC Comrade Ayuba Wabba, ya zargi gwamnatin tarayya da ministan kwadago, Sanata Chris Ngige na bata lokaci wajen sake fasalin albashi mafi karanci na ma'aikata; yana mai gargadin cewa hakurin ma'aikata ya kusa karewa.

KARANTA WANNAN: PDP ta tsaida Matawallen-Maradun a matsayin dan takararta na gwamnan jihar Zamfara

Hoto: Shugaban Kungiyar kwadago ta kasa, Comrade Wabba (Tsakiya)

Hoto: Shugaban Kungiyar kwadago ta kasa, Comrade Wabba (Tsakiya)
Source: Depositphotos

A ka'idar yarjejeniyar da aka kulla don kammala tattara bayanta, kwamitim da zai duba batun karin albashi mafi karanci wanda ya kunshi kungiyoyin kwadago, gwamnati da masu daukar aiki, sun kammala aikinsu a makon da ya gabata; sai dai akasin sakamakon da kungiyoyin kwadago suke jira, Ministan kwadago ya ce gwamnatin tarayya bata shirya karin albashi ba.

Wabba ya bayyana cewa jihohi sun aiko da takardun yarjejeniya, ya kara da cewa jihohi 12 daga cikin jihohi 21 da suka aiko da takardun yarjejeniyar sun bayyana karin albashi mafinkaranci, yayin da kungiyar masu daukar aiki NECA da kungiyoyin kwadaga suma suka fitar da nasu karin albashi mafi karancin.

Ya yi gargadin cewa wannan hukunci da gwamnati ta yanke ba zai yiwa ma'aikata dadi ba, yana mai karawa da cewa: "Wannan hukunci da suka dauka na cewa basu shirya kara albashi ba, sam bai yiwa ma'aikata dadi ba, don haka muma ya zama wajibi mu sanar da kusoshin wannan tafiya tamu. Mun yanke shawarar yin zama a mako mai zuwa, a nan ne zamu yanke namu hukuncin."

A baya Legit.ng ta ruwaito maku cewa Ministan kwadago Sanata Chris Ingege, ya sanar da cewa gwamnati ba ta shirya karin albashi a watan Satumba, yana mai dora alhakin hakan akan gazawar gwamnoni na bada yarjejeniyar karin albashi a jihohinsu.

Sanata Chris Ingige, wanda ya sanar da hakan a Anambra, ya ce har sai kowane bangare sun gabatar da nasu karin albashin, sannan ne gwamnati zata aikawa majalisun dokoki na kasa da kudurin sake fasalin albashi mafi karanci na ma'aikata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel