Gwamnan arewa ya ce bashi da N20m a asusun sa na banki

Gwamnan arewa ya ce bashi da N20m a asusun sa na banki

- Gwamna Nasir El-Rufai ya ce kudin da ke asusun ajiyarsa na banki bai kai N20m ba

- Gwamnan ya bayyana hakan ne bayan wasu kungiyoyi a jihar Kaduna sun saya masa fom din takarar

- Gwamnan ya mika godiyarsa ga kungiyoyin, ya kuma yi alkawarin cigaba da sharara musu romon demokradiya a jihar

Bani da N20m a asusun ajiyar banki na - El-Rufai

Bani da N20m a asusun ajiyar banki na - El-Rufai
Source: Original

A yau, Litinin, 3 ga watan Satumba ne gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya ce bashi da N20 miliyan da zai saya fom din takarar gwamna.

El-Rufai ya yi maganar ne lokacin da yake mika godiyarsa ga kungiyoyin masu sayar da shanu, da kungiyar dilalan man fetur (IPMAN) da kungiyoyar direbobi (NATO) da kuma kungiyar 'yan kasuwan Sheikh Gumi da suka saya masa fom din.

DUBA WANNAN: Tsohon gwamna ya sayi fam din takara daga gidan yari

Gwamnan ya ce, "Ba zan manta ba lokacin da jam'iyyar ta bayyana kudin fom din, Shugaban kasa ne mutum na farko da ya daga hannunsa ya ce bashi da N50m da zai sayi fom din.

"Hakan yasa, mu gwamnoni muka fara shawarwarin yadda za muyi karo-karo domin mu saya wa shugaban kasa fam.

"Munyi shawarar cewa kowanne gwamna zai kawo N20 miliyan. Sai dai lokacin da muka tafi China sai na fadawa shugaban kasa cewar wata kungiya ta saya masa fam din takarar. Ni kuma wane zai saya min?

"Bani da N20 miliyan da zan saya fom din takara. Kudin da nake da shi a asusun ajiya a GT Bank bai yi kusa da wannan adadin ba. Ba zan iya fitar da wannan kudin ba sai dai idan na sayar da gida na."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel