Lokaci yayi da za’a samu shugaban kasa da zamu iya alfahari dashi – Saraki

Lokaci yayi da za’a samu shugaban kasa da zamu iya alfahari dashi – Saraki

Shugaban majalisar Bukola Saraki yace yan Najeriya na bukatar shugaban kasa da zasu iya alfahari dashi.

Saraki wanda ke neman takaran kujeran shugaban kasa a zaben 2019 a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya bayyana hakan yayinda ya ziyarci diliget da shugabannin jam’iyyar a jihar Benue domin neman goyon bayansu.

Shugaban majalisar dattawa yace yana son zama shugaban kasar Najeriya na gaba saboda Najeriya na kan hanyar ballewa sannan kuma shi yana son hada kan kasar.

“Lokaci yaayi da za’a samu shugaban da zai iya mulki, lokaci yayi da za’a sam shugaba, idan ka ga shugaban kasa ya tsaya yana Magana, zaka ce ina alfahari da kasancewarsa shugaba na,” inji Saraki.

Lokaci yayi da za’a samu shugaban kasa da zamu iya alfahari dashi – Saraki

Lokaci yayi da za’a samu shugaban kasa da zamu iya alfahari dashi – Saraki
Source: Depositphotos

"Ina bukatar goyon bayanku domin zama dan takaran shugaban kasa a PDP sannan na zamo shugaban kasar jumhuriyar Najeriya na gaba. Lokaci yayi da zamu yi shugabanci. Lokaci yayi da ya kamata mu samar ma kasar nan shugaba.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Fashewar gas yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama a Nasarawa

“Kalla, idan kuna bukatar aboki, ina nan a koda yaushe domin na taimaki mutanen jihar Benue. Na nuna kuma zan ci gaba da nunawa, saboda Najeriya a yau tana kan hanyar ballewa. Muna bukatar hada kan kasar nan. Muna bukatar barin kowa ya san cewa Najeriya nasa ne."

Ya jadadda cewa lokaci yayi da ya kamata yan Najeriya su san adalci ta fannin daidaito.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel