2019: Sule Lamido zai janye mun a matsayin dan takara shugaban kasa a PDP - Atiku

2019: Sule Lamido zai janye mun a matsayin dan takara shugaban kasa a PDP - Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana a ranar Litinin, 10 ga watan Satumba cewa yayi imani abokin takaransa, Sule Lamido zai janye masa.

Lamido da Atiku na cikin masu neman tikitin tsayawa takaran shugabancin kasa a karkashin jam’iyyar Peples Democratic Party (PDP).

Mista Atiku ya bayyana hakan a ranar Litinin a hedkwatar PDP a Dutse, jihar Jigawa lokacin da ya gana da shugabannin jam’iyyar akan kamfen dinsa.

2019: Sule Lamido zai janye mun a matsayin dan takara shugaban kasa a PDP - Atiku

2019: Sule Lamido zai janye mun a matsayin dan takara shugaban kasa a PDP - Atiku
Source: Depositphotos

Yace yayi imanin Lamido zai bar masa tikitin saboda tsohon gwamnan kaninsa ne kuma suna da tunani iri guda ta fannin siyasa.

KU KAARANTA KUMA: Jerin sunayen yan takara da suka yanki fam din takaran gwamnan na APC da PDP a Nasarawa

Ya fadama taron cewa mahaifiyarsa yar asalin Jigawar Sark ice, wani kauye a karamar hukumar Dutse kafin su koma jihar Adamawa inda aka haife shi.

Yace Sule Lamido danuwansa ne don haka zaiyi koyi da abunda ya faru tsakanin Shehu Musa da danuwansa Uamaru Musa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel