Ku daina amfani da addini don son zuciyarku – Yar majalisa ta gargadi shugabannin addini

Ku daina amfani da addini don son zuciyarku – Yar majalisa ta gargadi shugabannin addini

- Aishat Dukku, mamba a majalisar wakilai ta gargadi shugabannin addini

- Ta gargade akan amfani da wa'azin batanci wajen yada rikici da kiyayya

- Ta kuma kara da cewa shugabannin addini su daina amfani da addini don son zuciyarsu

Aishat Dukku, shugaban majalisan wakilai kan harkokin zabe ta shawarci shuwagabannin addini da su kiyayi yin suka ko hare-hare akan jam’iyyun siyasa ko yan siyasa.

Dukku, ta bada shawarar ne a wani hira tare da kamfanin dillancin labarai (NAN) a ranan Litinin, 10 ga watan Satumba, a Abuja, ta bayyana cewa shuwagabannin addinai suyi amfani da matsayinsu wajen yada zaman lafiya.

Ku daina amfani da addini don son zuciyarku – Ýar majalisa ta gargadi shugabannin addini

Ku daina amfani da addini don son zuciyarku – Ýar majalisa ta gargadi shugabannin addini
Source: Depositphotos

“Baza a iya raba addini da harkar zabe ko na siyasa ba, ya rage garemu muyi amfani da addini ta hanyar da ta dace domin a ko wace addini akwai ka’idodi. Sabod haka muna bukatar shuwagabannin addinai dasu yi amfani da wadannan ka’idodin ta hanyar da ta dace don anfanar yan Najeriya da kuma ilimantar da mabiya.”

“Ina matukar adawa da wa’azin batanci; nayi imani babu limami ko faston day a kamata yayi wa’azin batanci saboda babu addinin da ya bukaci kowani shugaba da ya ingiza mbiyansa. Manyan addinan Najeriya sune addinin Kirista da na Islama sannan kuma akwai ka’idoji kan yadda addinan biyu zasu iya zaman lafiya a tare.”

KU KARANTA KUMA: Jerin sunayen yan takara da suka yanki fam din takaran gwamnan na APC da PDP a Nasarawa

Ta kuma yi kira ga yan siyasa da su daina amfani da addini don cimma wata manufa na gashin kansu, inda ta kara da cewa kamata yayi su nemi ra’ayin kasa baki daya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel