Abba Kyari: Shugaba Buhari yayi karya game da badakalar kwangiloli

Abba Kyari: Shugaba Buhari yayi karya game da badakalar kwangiloli

Bincike ya nuna cewa babu gaskiya a maganar da Fadar Shugaban kasa tayi na wanke Abba Kyari daga zargin karbar cin hanci wajen ba wani ‘Dan uwan sa kwangilar shigo da motoci.

Abba Kyari: Shugaba Buhari yayi karya game da badakalar kwangiloli

Hujjar cewa Gwamnatin Buhari ta bada kwangilar shigo da motoci
Source: Depositphotos

A jiya ne Garba Shehu wanda ke magana da yawun Shugaban kasa ya wanke Shugaban Ma’ikatan fadar Shugaba Buhari watau Abba Kyari inda yace babu inda Gwamnatin Tarayya ta bada kwangilar shigo da motoci a kaf kasafin 2016 da kuma 2017.

Sai dai binciken da Hukumar ICiR mai bin kwa-kwaf tayi ya nuna cewa tabbas akwai inda aka ware kudi domin shigo da motoci kirar Hilux a fadar Shugaban kasa. A bata Garba Shehu ya nuna cewa babu inda aka ware kudi domin a saye Hilux a bara.

KU KARANTA: Yarima ya ci girma ya kyale Yari yayi takaran Sanata

Abba Kyari: Shugaba Buhari yayi karya game da badakalar kwangiloli

Wata hujjar cewa Gwamnatin Buhari ta bada kwangilar shigo da motoci
Source: Depositphotos

Sai dai yanzu an fitar da hotuna da za su tabbatar da cewa ba shakka Gwamnati ta sa sayen motocin cikin kundin kasafin kudin 2016 da ma 2017. Sai dai ICiR ta bayyana mana cewa har yanzu Fadar Shugaban kasa Buhari ta hakikance a kan bakar ta.

A kasafin kudin 2016 da 2017, Gwamnatin Buhari ta ware kudi kusan Naira Miliyan 200 wajen shigo da manyan motoci kirar Marsandi, da Toyota, da kuma manyan motoci irin su; Land Cruiser, Prado jeeps, da kuma Hillux din da Peugeot 607 da sauran su.

Jiya kuma Fadar Shugaban kasa ta karyata rade-radin cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya ki sa hannu ne a kan kudirin da zai gyara dokar zabe saboda yana tsoron ayi amfani da na’urorin zamani a 2019. Shugaba Buhari yace ba haka lamarin yake ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel