Ku tabbatar kun kawo wa Buhari kuri’u sama da miliyan 5, shugaban APC ya fadama magoya baya a Kano

Ku tabbatar kun kawo wa Buhari kuri’u sama da miliyan 5, shugaban APC ya fadama magoya baya a Kano

- Magoya bayan APC na kokarin ganin sun yi kokari wajen nasarar Buhari

- An bukaci magoya bayan shugaban kasar a Kano su kawo masa kuri'a sama da miliyan biyar

- Shugaban APC a jihar ne ya daura masu wannan babban aikin

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas Sanusi ya bukaci mambonim jam’iyyar a jihar da su jajirce wajen kawo kuri’u sama da miliyan biyar da Gwamna Abdullahi Ganduje ya daukarma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari alkawari a zaben 2019 a jihar.

Sanusi yayi Magana ta bakin wakilinsa a ranar Lahadi, 9 ga watan Satumba a lokacin kaddamar da kungiyar magoya bayan APC na jihar a gidan gwamnatin jihar, jaridar Daily Sun ta ruwaito.

A cewar rahoton, taron ya ja hankalin masu ruwa da tsaki na APC da dama kamar tsohon dan takarar kujerar shugaban kasa a jam’iyyar NRC Alhaji Bashir Tofa, tsohon ministan kwadago Alhaji Musa Gwadabe da kuma tsohon ministar harkokin mata Hajia Aisha Ismail.

Ku tabbatar kun kawo wa Buhari kuri’u sama da miliyan 5, shugaban APC ya fadama magoya baya a Kano

Ku tabbatar kun kawo wa Buhari kuri’u sama da miliyan 5, shugaban APC ya fadama magoya baya a Kano
Source: Depositphotos

Shugaban jam’iyyar ya bayyana cewa ya je dukkanin lungu da sako na jihar don menawa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Gwamna Abdullahi Ganduje kuri’u kafin da lokacin zabe.

Ya bukaci da su tabbatar da cewa masu jefa wa Shugaba Buhari kuri’u sun kada kuri’unsu ga Gwamna Ganduje da sauran yan APC domin cewa jam’iyyar guda ce.

KU KARANTA KUMA: Garba Shehu yace adawa ne yasa aka zargi Kyari da cin hanci

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a bayan cewa Malam Abba Kyari, shugaban ma’aikatan Shugaba Buhari yayi barazanar maka wata kafar labarai ta kasa kotu akan wani labara dake zarginsa na karban cin hancin naira miliyan 29 don ya bayar da wani kwangila.

A wata sanarwa daga Malam Garba Shehu, kakakin shugaban kasar yace Kyari baida zabin day a rage illa na daukar matakin doka bayan jaaridar tayi watsi da sanar mata da akayi cewa labarin karya ne.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel