Raba kafa: 'Yan takarar PDP 3 sun sayi fam din takara 2

Raba kafa: 'Yan takarar PDP 3 sun sayi fam din takara 2

- Wasu daga cikin 'yan takara a jam'iyyar PDP sun raba kafa ta hanyar sayar fom din takara biyu

- An gano cewa sun saya fam din ne ta hanyar amfani da yaransu na siyasa

- Masu fashin baki na siyasa ne ganin cewa 'yan takarar sunyi haka ne saboda raba kafa ko da b suyi nasara a zaben fidda gwani ba

A kidaya ta karshe da aka yi, akwai mutum 14 dake takarar neman jam’iyyar PDP ta tsayar da su takarar shugaban kasa.

‘Yan takarar su ne, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar; tsohon shugaban majalisar dattijai, David Mark; shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki; gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal; gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo; tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa; tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Kwankwaso; tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido; tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ahmed Makarfi.

Ragowar sun hada da tsohon gwamnan jihar Filato, David Jang; tsohon ministan aiyuka na musamman, Tanimu Turaki; da kuma tsohon sanatan jihar Kaduna ta arewa, Datti Baba-Ahmed.

'Yan takarar shugabancin kasa 3 a PDP sun sayi fam din takarar gwamna da Sanata

'Yan takarar shugabancin kasa 3 a PDP sun sayi fam din takarar gwamna da Sanata
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Tsohon gwamna ya sayi fam din takara daga gidan yari

Sai dai a wani lamari da za a iya cewa tamkar na raba kafa saboda rashin tabbacin samun takarar shugabancin kasa, wasu masu neman jam’iyyar PDP ta tsaya da su takara sun sayi fam din kujerun da suke kai.

‘Yan takarar uku sun sayi fam din ta hanyar amfani da yaran su na siyasa kamar yadda majiyar Legit.ng ta tabbatar.

Dukkan ‘yan takarar na daga cikin ‘yan siyasar da suka canja sheka daga APC zuwa PDP kamar yadda majiyar mu bankado.

Duk da majiyar mu ba ta ambaci sunayen ‘yan takarar ba, ta sanar da mu cewar akwai gwamna daya da sanatoci biyu.

Gwamnonin jihohin Benuwe, Samuel Ortom, da na Sokoto, Aminu Waziru Tambuwal, suka bar canja sheka daga APC zuwa PDP.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel