Tsohon gwamna ya sayi fam din takara daga gidan yari

Tsohon gwamna ya sayi fam din takara daga gidan yari

- Daya daga cikin magoya bayan Sanata Joshua Dariye, Monday Shedrack Kopmut, ya wallafa hotunan fam din takarar zaben 2019 da ya ce tsohon gwamnan ya saya

- A halin yanzu sanatan yana garkame a gidan yari bayan kotu ta same shi da laifin almubazarranci da kudin jihar Filato har N1.16 biliyan

Wani rahoton da ba'a tabbatar da sahihancinsa ba ya ce Sanata Joshua Dariye da ke garkame a kurkuku bayan kotu da yanke masa hukuncin shekaru 14 ya sayi fam din takarar Sanata a yankin Filto na tsakiya karkashin jam'iyyar APC.

An yankewa Dariye hukuncin ne bayan kotu ta same shi da laifin karkatar da kudaden jihar Filato wanda adadinsu ya kai N1.16 biliyan.

Tsohon gwamna ya sayi fam din takara daga gidan yari

Tsohon gwamna ya sayi fam din takara daga gidan yari
Source: Depositphotos

Wani mai goyon bayan tsohon gwamnan na jihar Filato, Monday Shadrack Kopmut, ne ya wallafa hotunan fam din takarar dauke da Sunan Sanata Joshua Dariye a shafinsa na Facebook a ranar Asabar 8 ga watan Satumba.

DUBA WANNAN: Shugaban PDP na wata jiha a Kudu da magoya bayansa 5,000 sun sauya sheka zuwa APC

Shadrack ya rubuta, "Ina son in sanar da magoya bayan Sanata Dr Cif Joshua C. Dariye, cewa sanatan talakawan ya saya fam din takarar sanata na zaben 2019 a karkashin jam'iyyar APC saboda ya wakilci jama'an Filato ta Tsakiya a majalisar tarayya."

Ga sakon kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook.

A wani rahoton, Legit.ng ta kawo muku cewa wani masanin tattalin arziki, Dr Zuhumnam Dapel ya ce dalilan da yasa talauci ya fi tsananta a arewacin Najeriya fice da Kudu shine karancin kudaden shiga da jihohin arewa ke samu.

Sauran dalilan da ya lissafa sun hada da karancin ilimi, yawan haihuwa da satar kudaden jama'a da yan siyasa keyi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel