Garba Shehu yace adawa ne yasa aka zargi Kyari da cin hanci

Garba Shehu yace adawa ne yasa aka zargi Kyari da cin hanci

- Garba Shehu yace zargin cin hanci da ake yiwa Abba Kyari siyasa ce

- Hadimin shugaban kasa yace masu adawa da gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne suka kulla makircin

- An zargi shugaban ma’aikata, Abba Kyari da karban cin hancin naira miliyan 29

Babban mai ba shugaban kasa shawara a kafofin watsa labarai, Garba Shehu ya bayyana zargin cin hanci da ake yiwa shugaban ma’aikatan shugaban kasa, Abba Kyari a matsayin aiki wasu masu adawa da gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Channels ta ruwaito cewa Shehu ya bayyana hakan a wata hira da yayi da tasahr talbijin din a ranar Lahadi, 9 ga watan Satumba.

Legit.ng ta tattaro cewa an zargi shugaban ma’aikatan da karban cin hancin naira miliyan 29 domin ya bada wani kwangila.

Garba Shehu yace adawa ne yasa aka zargi Kyari da cin hanci

Garba Shehu yace adawa ne yasa aka zargi Kyari da cin hanci
Source: Depositphotos

A cewar Garba Shehu ana yiwa fadar shugaban kasa bita da kulli saboda zaben 2019 dake gabatowa.

Yace basu taba fuskantar zargin satar kudi ba shiyasa masu adawa ke son ganin sun danawa gwamnatin tarayya tarkon sharri.

KU KARANTA KUMA: Mune muka haddasa girgizan kasa, mazauna su sa ran ganin wadda yafi na da – Yan asalin Abuja

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a bayan cewa Malam Abba Kyari, shugaban ma’aikatan Shugaba Buhari yayi barazanar maka wata kafar labarai ta kasa kotu akan wani labara dake zarginsa na karban cin hancin naira miliyan 29 don ya bayar da wani kwangila.

A wata sanarwa daga Malam Garba Shehu, kakakin shugaban kasar yace Kyari baida zabin day a rage illa na daukar matakin doka bayan jaaridar tayi watsi da sanar mata da akayi cewa labarin karya ne.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel