Shugaban PDP na wata jiha a Kudu da magoya bayansa 5,000 sun sauya sheka zuwa APC

Shugaban PDP na wata jiha a Kudu da magoya bayansa 5,000 sun sauya sheka zuwa APC

Jigo a jam'iyyar PDP kuma tsohon kwamishinan Lafiya na jihar tare magoya bayansa 5,000 sun koma APC. Sauran wadanda suka koma APC din sun hada da Sir Godwin Idungafa, tsohon mataimakin ciyaman na karamar hukumar Ika da Mr Harry Eduo, tsohon kansila a karamar hukumar Ika da wani fittacen lauya kuma dan siyasa, Uyo Udom.

Jam'iyyar PDP reshen jihar Akwa Ibom tayi babban rashi a ranar Asabar da ta gabata sakamakon sauya shekar wani jigo na jam'iyyar da ke karamar hukumar Ika, Dr Francis Udoikpong.

Shugaban PDP na wata jiha a Kudu ya sauya sheka zuwa APC

Shugaban PDP na wata jiha a Kudu ya sauya sheka zuwa APC
Source: Facebook

Dr Udoikpong daya daga cikin jiga-jigan jam'iyyar kuma tsohon kwamishinan lafiya a jihar ya koma APC ne tare da magoya bayansa 5,000 cikinsu har da Sir Godwin Idungafa, tsohon mataimakin ciyaman na karamar hukumar Ika da Mr Harry Eduo, tsohon kansila a karamar hukumar Ika da wani fittacen lauya kuma dan siyasa, Uyo Udom.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa arewacin Najeriya ya fi kudanci talauci - Masanin tattalin arziki

Wannan na zuwa na bayan tsohon mataimakin Sufeta Janar na 'yan sanda, Udom Ekpoudom (murabus) da Obong Otu Robert Akpan daga karamar hukumar Etim Ekpo suma sun sauya sheka zuwa APC domin hada karfi da karfe tare da Sanata Godswill Akpabio.

Dr Udoikpong ya ce sun yanke shawarar ficewa daga PDP ne saboda gwamnatin gwaman Udom Emmanuel ta mayar da karamar hukumar Ika saniyar ware a jihar.

Ya yi Allah wadai kan yadda aka sanya sunayensu cikin yakin neman zaben gwamna Emmanuel ba tare da neman amincewarsa ba.

A yayin da yake karbar sabbin mambobin, Ciyaman din APC na jihar, Mr Ini Okopido ya ce yanzu karamar hukumar Ika ta zama na APC saboda sauya shekarsu tare da magoya bayansu. Ya kuma bayyana cewa APC za ta lashe zabukan da za'a gudanar nan gaba a jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel