Hankula sun kwanta a Gundumbali bayan harin da Boko Haram suka kai - CJTF

Hankula sun kwanta a Gundumbali bayan harin da Boko Haram suka kai - CJTF

- Mayakan Boko Haram sun kai hari a kauyen Gundumbali da ke jihar Borno a ranar Juma'a da ta gabata

- Sojojin Najeriya tare da 'yan JTF sun dakile harin inda suka fatattaki 'yan ta'adan bayan sunyi musayar wuta

- Tuni mazauna kauyen suka cigaba da harkokinsu kuma sun bayyana gamsuwarsu kan yadda Sojin suka dauki mataki

Bayan harin da mayakan Boko Haram suka kai a kwana-kwanan nan a garin Gundumbali da ke karamar hukumar Guzamala na jihar Borno, mazauna kauyen da wasu 'yan kato da gora wato Civilian JTF sun tabbatar da sun ce zaman lafiya ya samu a garin.

Mutane da yawa sun rasa rayyukansu bayan 'yan Boko Haram sanye da kayan sojoji sun kai hari a kauyen na Gundumbali kamar yadda Vanguard ta wallafa.

Hankula sun kwamta a Gundumbali bayan harin da Boko Haram suka kai - CJTF

Hankula sun kwamta a Gundumbali bayan harin da Boko Haram suka kai - CJTF
Source: Twitter

Mazana kauyen wanda abin ya faru a idanunsu sun ce mayakan Boko Haram daga Tafkiri sun kai hari a yammacin Juma'a amma Sojojin Najeriya sun fattaki 'yan ta'addan bayan sunyi musayar wuta.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa arewacin Najeriya ya fi kudanci talauci - Masanin tattalin arziki

A yayin da suke tabbatar da afkuwar harin, 'yan kungiyar JTF da ke kauyen sun tabbatar da cewa hankula sun kwanta kuma mutane sun cigaba da gudanar da harkokinsu kamar yadda suka saba.

"Tabbas 'yan Boko Haram sun kawo hari inda suka rika yin ruwan harsasai," a cewar wani dan JTF da ya nemi a boye sunansa.

"Amma tare da taimakon Sojin Najeiya, munyi nasarar dakile harin kuma muka fatattake su."

Wani dan acaba, Salisu Musa, ya ce harin ya sanya dole ya koma gida cikin gagawa amma ya kara da cewa a halin yanzu mutane suna cigaba da gudanar da harkokinsu kamar yadda suka saba.

Kazalika, wani mazaunin kauyen mai suna Musa Mohammed ya bayyana gamsuwarsa kan yadda Sojojin Najeriya suka fattaki 'yan ta'addan cikin gagawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel