Mune muka haddasa girgizan kasa, mazauna su sa ran ganin wadda yafi na da – Yan asalin Abuja

Mune muka haddasa girgizan kasa, mazauna su sa ran ganin wadda yafi na da – Yan asalin Abuja

- Yan asalin babban birnin tarayya sun yi ikirarin cewa su ne suka haddasa girgizan kasa da ya afku a makon da ya gabata

- Yan asalin yankin karashin kugiyar Coalition of FCT Indigenous Associations (CFCTIA) sunyi ikirarin cewa wasu bala'in na nan zuwa

- Hujjarsu shine cewa gwamnatin tarayya ta mayar dasu saniyar ware

Wasu yan asalin babban birnin tarayya karkashin kungiyar Coalition of FCT Indigenous Associations (CFCTIA), sun yi ikirarin cewa su ne suka haddasa girgizan kasa da ya afku a wasu yankunan babban birnin tarayyar kasa.

A wata sanarwa dauke da sa hannun kakakin kungiyar, Yunusa Ahmadu Yusuf, wadda aka akewa yan jarida a ranar Lahadi, 9 ga watan Satumba ya gargadi mazauna Abuja da su saurari Karin irin wadannan lamari a yankunan birnin, har sai dai idan gwamnatin tarayya tayi adalci da wariyar da ake nuna masu.

Mune muka haddasa girgizan kasa, mazauna su sa ran ganin wadda yafi na da – Yan asalin Abuja

Mune muka haddasa girgizan kasa, mazauna su sa ran ganin wadda yafi na da – Yan asalin Abuja
Source: Facebook

Jawabin ya gargadi fadar shugaban kasa musamman Aso Villa da su tsimayi girgizan kasa, idan har ba’a nada dan asalin yankin a matsayin minister ba tsakanin yanzu zuwa Oktoba, 2018.

Ya bayyana irin wasu hukumomin gwamnati da jami’ai da suka ce girgizan kasar ya faru bisa yanayi ne a matsayin abun dariya, inda ya kara da cewa yan asalin yankin sun kasance masu zaman lafiya, amma sun tunzura saboda ba’a dauki zaman lafiyan nasu a bakin komai ba face mayar dasu saniyar ware da aka yi.

KU KARANTA KUMA: 2019: Da Buhari ya sani yaki amincewa da N45m na kudin fam din APC – Tsohon jami’in INEC

A baya munji cewa jama’a su shiga halin firgici da tashin hankali yayin da aka samu wata karamar girgizan kasa na tsawon dakika 30 zuwa 40 a babban birnin tarayya Abuja, kamar yadda jaridar This Day ta bayyana a cikin rahotonta.

Legit.ng ta kalato cewa wannan lamari ya faru ne a daren Laraba, 5 ga watan Satumba, inda mazauna unguwannin Mpape da Maiatama duk sun shaida da kuma tabbatar da faruwar lamarin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel