Kamata yayi ‘Yan Najeriya su rika jinjinawa Buhari – Minista Ngige

Kamata yayi ‘Yan Najeriya su rika jinjinawa Buhari – Minista Ngige

Ministan kwadago na Najeriya Chris Ngige ya bayyana cewa kamata yayi ace ‘Yan Najeriya su na tafawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari saboda irin kokarin da yake yi na gyara kasar nan.

Kamata yayi ‘Yan Najeriya su rika jinjinawa Buhari – Minista Ngige

Ministan kwadago Ngige yace da mamaki ace ba a ganin kokarin Buhari
Source: Twitter

Dr. Chris Ngige yake kuma cewa ya kamata ‘Yan Kasar su jinjinawa ‘Yan siyasar su kayi kokari wajen ganin Buhari ya karbi ragamar kasar nan. Dr. Ngige ya jero dalilan da su ka sa ya kamata a godewa irin kokarin da Shugaban kasa Buhari yake yi.

Ngige yake cewa lokacin da Buhari ya karbi mulki, gangar mai ya koma Dala 37 kacal a Duniya. Bayan haka kuma an samu tsageru su na fasa bututun mai har ta kai abin da ake iya hakowa a rana bai wuce ganga 600,000 maimakon akalla 2,200,000.

KU KARANTA:Akwai masu yi wa Buhari aiki cikin ‘Yan takarar PDP – Gwamnan Ribas

Ministan ya kuma nuna cewa yanzu Najeriya ce ta biyu a Duniya bayan Kasar Amurka wajen noman dawa. Bayan nan kuma Ministan yace yanzu Gwamnatin Najeriya ta daina kashe Dalolin Biliyoyi wajen shigo da shinkafa kamar yadda ake yi a baya.

A da dai Najeriya na kashe Dala Miliyan 5 a kowace rana wajen shigo da shinkafa daga waje. A shekara Gwamnati na kashe Dala Biliyan 1 wajen shigo da shinkafa inji Ministan. Ngige yayi wannan bayani ne a gaban ‘Yan jarida a Jihar Anambra.

Kwanaki ne Ministan kwadago na kasa Chris Ngige yayi magana game da albashin Ma’aikata a Najeriya inda yace Shugaban kasar ya damu da lamarin da ke kasa ya kuma ce za ayi wani abu

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel