2019: Da Buhari ya sani yaki amincewa da N45m na kudin fam din APC – Tsohon jami’in INEC

2019: Da Buhari ya sani yaki amincewa da N45m na kudin fam din APC – Tsohon jami’in INEC

- Naira miliyan 45 na kudin fam din takaran kujerar shugabancin kasa a APC na ci gaba da haifar da cece-kuce

- Wani tsohon kwamishinan hukumar INEC, Farfesa Lai Olurode, yace farashin ya kori sauran masu son yin takara kai tsaye

- Yace da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sani bai amince da farashin ba

Wani tsohon kwamishinan hukumar INEC, Farfesa Lai Olurode, a ranar Lahadi, 9 ga watan Satumba yace da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yaki amincewa da naira miliyan 45 da jam’iyyar APC ta tsayar a matsayin farashin fam din takaran shugaban kasa na zaben 2019.

Yace hukuncin APC ya kori sauran yan takara musamman matasa da bazasu iya samun kudin siyan fam din takaran ba.

2019: Da Buhari ya sani yaki amincewa da N45m na kudin fam din APC – Tsohon jami’in INEC

2019: Da Buhari ya sani yaki amincewa da N45m na kudin fam din APC – Tsohon jami’in INEC
Source: UGC

Farfesan ya bayyana hakan a Lagas a lokacin taron kungiyar dalibai musulmai na kasa da ake yi duk shekara a, sashin jihar Lagas, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ya kuma koka akan yawan matsaloli na siyan kuri’u wadda ya bayyana a matsayin abunda ya sabama addinin Musulunci yayinda ya bayyana hakan a matsayin siyar da yancin kai.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa fadar Shugaban kasa ta karyata rade-radin cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya ki sa hannu ne a kan kudirin da zai gyara dokar zabe saboda yana tsoron ayi amfani da na’urorin zamani a zaben da za ayi a shekara mai zuwa 2019.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Boko Haram sun sake kai sabon hari sansanin sojoji a Borno

Garba Shehu wanda shi ne ke magana da bakin Shugaban kasa Buhari ya bayyana cewa Shugaban kasar yana cikin masu son ganin an yi amfani da na’u’rorin zamani watau “Card Reader” a zabe mai zuwa akasin yadda wasu ke ta fada a kasar.

Mai magana da yawun Shugaban kasar yayi wannan jawabi ne jiya inda yayi karin haske game da dalilin da ya sa Shugaba Buhari bai amince da kudirin yi wa tsarin zabe garambawul da Majalisar Tarayya ta kawo masa ba kwanakin baya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel