Ba na gudun ayi amfani da na’u’rorin zamani a zaben 2019 – Shugaban kasa Buhari

Ba na gudun ayi amfani da na’u’rorin zamani a zaben 2019 – Shugaban kasa Buhari

Fadar Shugaban kasa ta karyata rade-radin cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya ki sa hannu ne a kan kudirin da zai gyara dokar zabe saboda yana tsoron ayi amfani da na’urorin zamani a zaben da za ayi a shekara mai zuwa 2019.

Ba na gudun ayi amfani da na’u’rorin zamani a zaben 2019 – Shugaban kasa Buhari

Buhari yace akwai gyara a kudirin da Majalisa ta ba shi na canza dokar zabe
Source: UGC

Garba Shehu wanda shi ne ke magana da bakin Shugaban kasa Buhari ya bayyana cewa Shugaban kasar yana cikin masu son ganin an yi amfani da na’u’rorin zamani watau “Card Reader” a zabe mai zuwa akasin yadda wasu ke ta fada a kasar.

Mai magana da yawun Shugaban kasar yayi wannan jawabi ne jiya inda yayi karin haske game da dalilin da ya sa Shugaba Buhari bai amince da kudirin yi wa tsarin zabe garambawul da Majalisar Tarayya ta kawo masa ba kwanakin baya.

Shugaban kasar yace bai taba tsoron ayi amfani da na’urorin zamani ba kuma babu abin da zai hana ayi amfani da su a zaben 2019. Buhari yace bai amince da kudirin bane saboda wasu abubuwa da Majalisa ta sa cikin dokar kuma ya nemi a gyara.

KU KARANTA: 'Yan adawa ne kar zargin Buhari da cin hanci - Garba Shehu

A bayanin Shugaban kasar ya bayyana cewa ya sha kasa a zabuka har sau 3 don haka ya san amfanin da na’urar tayi masa a zaben 2015. Shugaba Buhari yace tuni an gama maganar aiki da na’urorin nan a zabe illa wasu ‘Yan gyara-gyare da za ayi.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kuma nuna cewa babu rikici tsakanin sa da Majalisar kasar a kan wannan lamari duk da sau 3 ana neman ya sa hannu a dokar da ta ke neman ayi wa tsarin zaben Najeriya garambawu amma har yau bai yi ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel