2019: Jam’iyyar APC ta caccaki Atiku Abubakar da David Mark

2019: Jam’iyyar APC ta caccaki Atiku Abubakar da David Mark

Jam’iyyar APC mai mulki ta tambayi tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ya fadawa Duniya abin da ya hana sa gyara kasar nan lokacin yana kam karagar mulki na shekaru 8.

2019: Jam’iyyar APC ta caccaki Atiku Abubakar da David Mark

APC tace akwai lauje cikin nadi a shirin su Atiku Abubakar
Source: Depositphotos

Atiku Abubakar yana cikin masu neman takarar Shugaban kasa a Jam’iyyar PDP inda yake alkawarin cewa zai yi wa Najeriya garambawul idan har ya samu mulki. Hakan ya sa APC ta ke ganin akwai alamun yaudara a lamarin na Atiku Abubakar.

Yekini Nabena wanda shi ne Sakataren yada labarai na APC yayi jawabi jiya a madadin Jam’iyyar inda yace su na mamakin abin da ya hana Atiku dabbaka tsarin da yake kira a yau na yi wa fasalin kasa garambawul a lokacin yana mulkin Najeriya.

APC tace dadin baki ne Atiku yake yi domin kuwa yayi Mataimakin Shugaban kasa na tsawon shekaru 8 inda Jam’iyyar tace da ace da gaske yake yi game da kiran sa na sauya fasalin kasa da a wancan lokaci yayi kokarin yi wa Najeriyar garambawul.

KU KARANTA: Wasu 'Yan takarar PDP da zargin satar kudi ya hana sukuni

Sakataren yada labaran ya kuma caccaki Sanata David Mark wanda yana cikin masu neman kujerar Shugaban kasa a PDP a 2019. Nabena yace Mark ya rike Majalisar Dattawa na shekaru 8 amma bai taba kawo kudirin yi wa kasar garambawul ba.

APC ta nemi a daina yaudarar al’umma ana siyasantar da maganar sakewa Kasar nan fasali domin a cin ma burin 2019. Jam’iyyar tace za tayi aiki da abin da wani kwamiti karkashin Gwamna Nasir El-Rufai ta fitar domin sake fasalin tsarin Najeriya.

Jiya dai kun ji cewa tsohon Gwamnan Kano Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa ba zai yi takarar kujerar Shugaban kasa da Buhari a 2019 ba. Shekarau yana cikin masu neman Shugaban kasa a PDP kafin ya sauya sheka zuwa APC a makon jiya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel