Ana musayar kalamai tsakanin APC da Gwamnan Ribas game da zaben 2019

Ana musayar kalamai tsakanin APC da Gwamnan Ribas game da zaben 2019

- Gwamna Wike yace akwai wasu da ke yi wa Buhari aiki a cikin PDP

- Wike yace akwai wadanda ke tare da APC cikin ‘Yan takarar PDP

- APC ta dai maidawa Gwamnan martani inda tace ya daina sambatu

Ana musayar kalamai tsakanin APC da Gwamnan Ribas game da zaben 2019

APC tace Wike ya fadi masu yi wa Buhari aiki a cikin PDP
Source: Depositphotos

Mun samu labari cewa Gwamnan Jihar Ribas Nyesom Wike ya zargi Jam’iyyar APC da kuma Shugaban kasa Muhammadu Buhari da aiki da wasu ‘Yan takarar Shugaban kasa a PDP domin jefa Jam’iyyar cikin rikici a zabe mai zuwa na 2019.

Jam’iyyar APC ta Jihar Ribas ta maidawa Gwamna Nyesom Wike martani bayan ya zargi Uwar Jam’iyyar da kokarin yi wa PDP zagon-kasa a 2019. Jam’iyyar ta APC ta kalubalanci Gwamnan ya fadi sunan masu yi wa APC aiki a PDP.

KU KARANTA: 2019: Daya daga cikin masu takaran PDP ya janye

APC ta nemi Gwamnan ya fadawa Duniya wadanda su ke aiki da APC da kuma Shugaba Buhari a boye cikin Jam’iyyar adawar ta PDP. APC ta Ribas dai ta caccaki babban Gwamnan na PDP inda tace PDP ta fadi zaben 2019 ta gama.

Kamar yadda mu ka samu labari daga Premium Times Jam’iyyar ta APC da ke mulkin kasar nan kuma ta nemi ‘Yan siyasar da ke kokarin ganin cigaban kasar nan su tattara ina-su ina-su su bar PDP su dawo APC domin a tsira tare.

Yayin da ake buga gangen zaben 2019, kun ji cewa Gwamna Ibrahim Dankwambo ya kara jan kunnen Jam’iyyar PDP wajen tsaida ‘Dan takaran 2019 inda yace ana tuna wadanda ba su taba sauya sheka ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel