Cin hanci: Wani na hannun Jonathan na neman jefa shi da matar sa cikin tsomomuwa

Cin hanci: Wani na hannun Jonathan na neman jefa shi da matar sa cikin tsomomuwa

- Wani na hannun Jonathan na neman jefa shi da matar sa cikin tsomomuwa

- Ya ce shi fa dukkan kudaden da ake bincikar sa da ci, sa shi akayi

Mataimaki na musamman akan harkokin cikin gida ga tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan lokacin mulkin sa mai suna Dakta Waripamo-Owei Dudafa, a jiya ya kara jadda cewa shi fa dukkan kudaden da ake bincikar sa da ci, sa shi akayi.

Cin hanci: Wani na hannun Jonathan na neman jefa shi da matar sa cikin tsomomuwa

Cin hanci: Wani na hannun Jonathan na neman jefa shi da matar sa cikin tsomomuwa
Source: Depositphotos

KU KARANTA: An karyata batun karin alawus na masu yi wa kasa hidima

Dakta Waripamo-Owei Dudafa ya bayyana cewa tsohon shugaban kasar Dakta Goodluck Jonathan da matar sa Patience Goodluck sune suka sa shi ya cire kudaden kuma yana ganin ya kamata ayi masa adalci.

Legit.ng ta samu cewa ana tuhumar Dakta Waripamo-Owei Dudafa da wani na hannun damar sa mai suna Iwejuo Nna Joseph a wata babbar kotun tarayya a garin Legas bisa yin sama da fadi da Naira biliyan 1 da dubu dari shidda.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa an gurfanar da wadanda ake tuhumar a kotun a baya tun cikin watan Yunin shekarar 2016 akan zargin da ake yi masu, inda su kuma suka musanta zarge-zargen.

A wani labarin kuma, Wani lamari mai cike da sarkakkiyar ban al'ajabi ya auku a garin Awo Idemili na jihar Anambara dake a shiyyar kudu maso gabashin kasar nan inda amarya ta haifi sambalelen saurayi kimanin awa biyu kafin a daura mata aure.

Ita dai amaryar mai suna Misis Chinezu Adeolisa ta bayyana wa duniya farin cikinta na samun sankacecen jariri a ranar ɗaurin aurenta da rabin ranta Mista Odeolisa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel