An soke bangaren kwararru na hukumar 'yansanda saboda samame da suke kaiwa

An soke bangaren kwararru na hukumar 'yansanda saboda samame da suke kaiwa

- An soke Police Special Tactical Squad (STS)

- Za'a hadawa sauran yan sanda aiyukan su

- Hakan ya biyo bayan bincike gidan Mista Clark da sukayi

An soke bangaren kwararru na hukumar 'yansanda saboda samame da suke kaiwa

An soke bangaren kwararru na hukumar 'yansanda saboda samame da suke kaiwa
Source: Twitter

Sifeto Janar na yan sanda, Ibrahim Idris, ya shafe STS na yan sanda, Helkwata jami'an ta sanar a ranar juma'a.

Wannan ya biyo bayan bincike gidan Edwin Clark da sukayi.

A sakamakon hakan ne duk jami'an da suke karkashin STS suka koma karkashin bangaren bincike na yan sanda.

Kamar yanda majiyar mu ta fada, daga bakin Jimoh Moshood, mataimakin kwamishinan yan sanda, yace sashen STS sun koma karkashin sashin bincike na yan sanda "

Wannan ya biyo bayan binciken gidan Mista Clark da ke Asokoro da jami'an suka yi. Yace jami'an basu samu damar hakan ba kafin su aiwatar, wanda Mista Idris yace basu bi ka'ida ba, kuma ba da yawun shi ba.

DUBA WANNAN: Kwankwaso ya kore ni daga PDP

Uku daga cikin jami'an hudu da sukayi binciken, an kore su jiya. Dayan kuma an dakatar dashi saboda ana cigaba da binciken rawar da ya taka.

Mista Idris ya tura manyan yan sanda tare da mataimakin sifeto Janar don ba wa Mista Clark hakuri.

Mista Clark yace ya hakura da abinda yan sandan sukayi mishi Amma yace tabbas daga sama ne aka turo su. Inda har yanzu hukumar yan sandan sun Musa hakan.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel