Gwamnatin Kaduna ta ware N3b don ilimin yara mata a jihar

Gwamnatin Kaduna ta ware N3b don ilimin yara mata a jihar

- Gwamnatin jihar Kaduna zata kashe Naira biliyan 3 akan ilimin yara mata

- Za'a yi amfani da kudin gurin daukar nauyin karatun yara mata na firamare

- Kudin na daga cikin dala miliyan 100 da bankin duniya ta bawa jihar

Gwamnatin Kaduna ta ware N3b don ilimin yara mata a jihar

Gwamnatin Kaduna ta ware N3b don ilimin yara mata a jihar
Source: UGC

Gwamnatin jihar Kaduna zata kashe Naira biliyan 3 akan ilimin yara mata da habaka makarantu kafin karshen 2018.

Dahiru Anchau, daraktan makarantun gwamnati a ma'aikatar ilimi, kimiyya da fasaha na jihar ya bayyana hakan a tattaunawar shi da ofishin dillancin labarai a ranar juma'a a Kaduna.

DUBA WANNAN: KannyWood: An shirya Ali Nuhu da Zango

Mista Anchau yace za'ayi amfani da kudin gurin daukar nauyin karatun yara mata a firamare da kuma horar da malamai mata na makarantun gwamnati.

Kamar yadda yace, kudin na daga cikin dala miliyan 100 na karkashin hadaka ta duniya a fannin ilimi (GPE). An raba kudin daga bankin duniya ga jihohin Kaduna, Kano, katsina, jigawa da Sokoto sakamakon rashin ilimin yara mata a jihar.

Ya bayyana cewa manufar su itace karfafa ingancin ilimi ga yara mata.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel