Da dumin sa: 'Yan majalisar tarayya sun dage ranar dawowar su daga hutu

Da dumin sa: 'Yan majalisar tarayya sun dage ranar dawowar su daga hutu

- 'Yan majalisar tarayya sun dage ranar dawowar su daga hutu

- Yanzu sai zuwa cikin sati na biyu a cikin watan Oktoba mai kamawa

- A da kuma 25 ga watan Satumba da muke ciki

'Yan majalisar tarayyar Najeriya mun samu labarin cewa sun dage ranar dawowar su hutun da suka tafi daga 25 ga watan Satumba da muke ciki har zuwa cikin sati na biyu a cikin watan Oktoba mai kamawa.

Da dumin sa: 'Yan majalisar tarayya sun dage ranar dawowar su daga hutu

Da dumin sa: 'Yan majalisar tarayya sun dage ranar dawowar su daga hutu
Source: Depositphotos

Wasu 'yan majalisar daga bangaren zauren dattawa da kuma wakilai da wakilin majiyar mu ya zanta da su sun bayyana cewa ranar dawowar ta su ta farko da suka sa kawo yanzu ta tabbata ba zata yiwuba .

Legit.ng ta samu cewa 'yan majalisar sun bayyana cewa a wannan lokacin da yawa daga cikin su ba za su samu damar dawowar ba saboda harkokin siyasa irin su zabukan fitar da gwani da suka rigaya suka soma kankama.

Wasu ma dai na ganin babu yadda za'ayi majalisar ta tabuka wani abu alhalin hankulan su duka yana a kan zabukan da ke gaban su a jam'iyyun su daban daban.

A wani labarin kuma, Shugaban hukumar nan dake kula da matasa masu yiwa kasa hidima watau National Youth Service Corps (NYSC) a turance mai suna Birgediya Janar Sale Zakari Kazaure ya ce karya ne batun karin alawus din da aka ce gwamnati tayi wa matasan.

Birgediya Janar Sale Zakari ya kara da cewa masu yiwa kasa hidima tamkar ma'aikata suke a tarayyar Najeriya don haka dole ne sai gwamnati ta amince da karin albashin ma'aikata sannan ne suma nasu alawus din zai samu kari.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel