Ba wannan maganar: Shugaban masu yiwa kasa hidima ya karyata batun karin alawus

Ba wannan maganar: Shugaban masu yiwa kasa hidima ya karyata batun karin alawus

- Shugaban masu yiwa kasa hidima ya karyata batun karin alawus

- Yace sai an karawa ma'aikata albashi sannan suma za su samu kari

- Ya shawarce su su zamo masu bin doka da oda

Shugaban hukumar nan dake kula da matasa masu yiwa kasa hidima watau National Youth Service Corps (NYSC) a turance mai suna Birgediya Janar Sale Zakari Kazaure ya ce karya ne batun karin alawus din da aka ce gwamnati tayi wa matasan.

Ba wannan maganar: Shugaban masu yiwa kasa hidima ya karyata batun karin alawus

Ba wannan maganar: Shugaban masu yiwa kasa hidima ya karyata batun karin alawus
Source: Facebook

KU KARANTA: Sarkin musulmi ya soki gwamnatin Buhari a kaikaice

Birgediya Janar Sale Zakari ya kara da cewa masu yiwa kasa hidima tamkar ma'aikata suke a tarayyar Najeriya don haka dole ne sai gwamnati ta amince da karin albashin ma'aikata sannan ne suma nasu alawus din zai samu kari.

Legit.ng ta samu cewa Birgediya Janar Sale Zakari yayi wannan bayanin ne a lokacin da yake jawabi ga sabbin masu yi wa kasa hidimar dake a sansanin horo na Issele-Uku, jihar Delta dake a shiyyar kudu maso kudancin Najeriya.

Daga karshe ya kuma ja hankalin masu yiwa kasa hidimar da su zamo masu da'a da kuma bin doka da oda a lokacin zaman su sansanin horon da ma wuraren da za'a kaisu.

A wani labarin kuma, 'Yan majalisar tarayyar Najeriya mun samu labarin cewa sun dage ranar dawowar su hutun da suka tafi daga 25 ga watan Satumba da muke ciki har zuwa cikin sati na biyu a cikin watan Oktoba mai kamawa.

Wasu 'yan majalisar daga bangaren zauren dattawa da kuma wakilai da wakilin majiyar mu ya zanta da su sun bayyana cewa ranar dawowar ta su ta farko da suka sa kawo yanzu ta tabbata ba zata yiwuba .

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel