Siyasar Kano: Shugabannin PDP sun jadadda goyon-baya ga Kwankwaso

Siyasar Kano: Shugabannin PDP sun jadadda goyon-baya ga Kwankwaso

Yayin da tsohon Gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau ya fice daga Jam’iyyar PDP zuwa APC mai mulki, Shugabannin Jam’iyyar adawar sun nuna goyon-bayan su ga Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Jiga-jigan Jam’iyyar adawa ta PDP har su 82 na Jihar Kano sun nuna cikakken goyon-bayan ga tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso. Manyan Jam’iyyar sun kai wa Sanatan ziyara ne a gidan sa da ke Garin Kaduna jiya Asabar.

Siyasar Kano: Shugabannin PDP sun jadadda goyon-baya ga Kwankwaso

Shugabannin PDP na Kano tare da Kwankwaso a Kaduna
Source: Depositphotos

Daga cikin wadanda su ka ziyarci ‘Dan takarar Shugaban kasar domin nuna mubaya’ar su akwai shugabannnin Jam’iyya 41 na Kananan Hukumomi. Haka kuma akwai Sakatarorin Jam’iyyar har 38 a cikin wannan babbar Tawaga.

A cikin ‘yan kwanakin nan ne Jam’iyyar adawar ta gamu da rashin bayan ficewar Ibrahim Shekerau. Malam Shekarau yace ba ayi masu adalci a PDP ba. Bayan an fifita ‘Yan Kwankwasiyya da su ka dawo Jam’iyyar adawar.

KU KARANTA: 2019: Wani mai neman takarar Shugaban kasa a PDP ya janye

Dama kun san cewa Shugaban PDP na Kasa Uche Secondus ya rusa shugabancin Jam’iyyar a Kano inda ya nada kwamitin rikon kwarya karkashin Dr. Rabiu Sulaiman Bichi da wasu mutane 6 da da-dama ke tare da Kwankwaso.

Mun kuma ji cewa jirgin yakin neman zaben Kwankwaso ya shiga Kasar Yarbawa inda har ya gana da ‘Dan takarar Gwamnan Jihar Osun a karkashin Jam’iyyar PDP a zaben da za ayi a watan nan Sanata Nuraddeen Adeleke.

'Daya daga cikin Hadiman ‘Dan takarar Shugaban kasar watau Hon. Saifullahi Hassan ne ya bayyana mana wannan a shafin sa na sadarwa na zamani na Tuwita lokacin da ake wannan muhimmin taro a gidan ‘Dan siyasar.

Tsohon Ministan ilmi na kasar ya dai bayyana irin rigimar da ta sa ya fice daga Jam’iyyar PDP inda yace ba ayi masu adalci ba. Tsohon Gwamnan na Kano yace PDP ta nuna son kai kararar inda ta fifita ‘Yan Kwankwasiyya da karfi da yaji a Jihar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel