Na yi aiki da Obasanjo, Jonathan da kuma ‘Yaradua a Gwamnati – Dankwambo

Na yi aiki da Obasanjo, Jonathan da kuma ‘Yaradua a Gwamnati – Dankwambo

- Dankwambo ya bayyana dalilin da ya sa ya dace da mulkin kasar nan

- Gwamnan yayi alkawarin nada Ministoci da zarar ya dare kan kujera

- ‘Dan takarar Shugaban kasar yace yayi aiki da tsofaffin Shugabanni 3

Na yi aiki da Obasanjo, Jonathan da kuma ‘Yaradua a Gwamnati – Dankwambo

Dankwambo yace shi kadai ne yayi aiki da Obasanjo, Jonathan da kuma ‘Yaradua
Source: UGC

Mun samu labari cewa Gwamnan Jihar Gombe Ibrahim Dankwambo wanda yake neman a zabe sa a matsayin ‘Dan takarar Shugaban kasa a Jam’iyyar PDP a 2019 ya bayyana dalilin cancantar sa da kuma inda zai sha-ban da Shugaba Buhari.

Dr. Ibrahim Dankwambo ya kuma bayyana dalilin da ya sa ya ke ganin ya cancanci mulkin Najeriya a 2019. ‘Dan takarar yayi wannan bayani ne a shafin sa na Tuwita inda yace yayi aiki da Shugabannin kasa 3 a Gwamnatin Tarayya.

KU KARANTA: Dankwambo ya ja kunnen Jam’iyyar PDP wajen tsaida ‘Dan takaran 2019

Dankwambo yayi aiki tare da tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo da kuma Marigayi Shugaba Ummaru ‘Yaradua da kuma Goodluck Jonathan a matsayin babban Akanta Janar na Najeriya lokacin Gwamnatin Jam’iyyar PDP.

Gwamnan ya hakikance cewa ya fi kowa dacewa da mulkin Kasar nan inda ya kuma yi alkawarin nada Ministoci da sauran Mukarraban sa. Gwamnan dai yana ikirarin cewa yana da Digiri fiye da 10 don haka ya san yadda zai gyara kasar nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel