Babu wata rigima tsakani na da Shugaba Buhari inji Shekarau

Babu wata rigima tsakani na da Shugaba Buhari inji Shekarau

Jim kadan da barin tsohon Gwamnan Kano Ibrahim Shekarau PDP zuwa APC, yayi doguwar hira da Daily Trust inda bayyana cewa ba zai yi takarar kujerar Shugaban kasa da Buhari a 2019 ba. Shekarau yana cikin masu neman Shugaban kasa a PDP.

Babu wata rigima tsakani na da Shugaba Buhari inji Shekarau

Buhari ya fara daga hannun Shekarau a siyasa amma su ka nemi kujera tare a 2011
Source: Depositphotos

Tsohon Gwamna Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa babu wata rigima tsakanin sa da Shugaba Buhari kai-tsaye sai dai ya koka da cewa akwai wasu daga Kano da su ka katange Shugaban kasar da su ka haddasa rikici tsakanin su.

Malam Shekarau yace yanzu haka Buhari ya rabu da duk wadannan mutane da su ka jawo rikici tsakanin sa da shi. Shekarau yace ya shiga APC ne kamar kowani gama-gari kuma zai yi wa Shugaban kasa biyayya a matsayin sa na babba.

KU KARANTA: Gwamnan Legas Ambode ya ce bai fice daga Jam'iyyar ba

Ibrahim Shekarau ya nuna cewa lokaci ne ke tsaida takarar Shugaban kasa inda ya nuna cewa a yanzu ba zai nemi kujerar Shugaba Buhari ba. Sai dai ana kishin-kishin din cewa APC za ta ba Shekarau takarar kujerar Sanatan Kano ta tsakiya a 2019.

Tsohon Ministan ilmi na kasar ya dai bayyana irin rigimar da ta sa ya fice daga Jam’iyyar PDP inda yace ba ayi masu adalci ba. Tsohon Gwamnan na Kano yace PDP ta nuna son kai karara inda ta fifita ‘Yan Kwankwasiyya da karfi da yaji a Jihar.

Bayan shigowar Kwankwaso PDP ne aka rusa shugabannin Jam’iyyar a Kano. Wannan abu da Jam’iyyar PDP tayi ne ya jawo Shekarau da Magoya bayan sa da sauran manyan ‘Yan siyasar Kano su ka fusata har ta Shekarau ya koma APC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel